Wani bawan Allah ya daba wa dan Acaba makami har lahira kan ya buge masa Kare
- Jami'an yan sanda sun cafke wani matashi, Ibrahim Sa'idu, da ya halaka ɗan Acaba da makami kan ya yi kuskuren kade masa kare a Gombe
- Kwamamishinan yan sandan jihar, Ishola Babaita, ya ce Karen da aka buge bai mutu ba, kuma mai laifin ya amsa tuhumar da ake masa
- Haka nan, yan sanda sun kama wasu mutane da ake zargi da garkuwa da mutane, an kwato makamai a hannun su
Gombe - Rundunar yan sanda reshen jihar Gombe tace ta kama wani Ibrahim Sa'idu, dan shekara 25 bisa zargin daba wa Dan Acaba, Saleh Babayo, makami har lahira.
Daily Trust ta rahoto cewa Matashin ya ɗauki wannan matakin ne bayan ɗan Acaban ya yi kuskuren buge masa Kare kuma Karen bai mutu ba.
Kwamishinan yan sandan jihar, Ishola Babaita, a wani taron manema labarai a Gombe, ya ce yan sandan Caji Ofis ɗin Akko ne suka damƙe Sa'idu a wurin da lamarin ya auku.
A kalamansa CP ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Saidu ya fusata har ta kai ga ya daba wa Saleh Babayo wuƙa, kuma hakan ya yi sanadin mutuwarsa, kawai saboda Mamacin ya yi kuskuren buge masa Kare.
Kwamishinan yan sandan ya yi bayanin cewa na ɗauki Babayo zuwa babban Asibitin Kumo, inda likitoci suka tabbatar da rai ya yi halinsa.
Ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, kuma ba da jimawa ba za'a gurfanar da shi a gaban Kotu.
Rahoto ya nuna cewa Karen da Mamacin ya kaɓe ya tsira da rayuwarsa kuma tare aka shigar da su cikin hedkwatar yan sanda.
Mun kama masu garkuwa - CP
Babaita ya ce dakarun yan sanda sun damke mutum 5 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, yayin da aka kama mutum biyu da zargin cin zarafi da fyaɗe.
Bugu da ƙari ya faɗi makaman da aka kwato a hannun su da suka haɗa da bindiga AK-47 da alburusai uku.
A cewarsa, nan ba da jimawa baki ɗaya waɗan da ake zargin za'a mika su gaban Kotu domin ta yanke musu hukunci.
A wani labarin kuma An tsinci gawar mai haɗa wa Mataimakin shugaban ƙasa takalmi a daki a Abuja
Omale Ojima mai haɗa Takalma a babban birnin tarayya Abuja, ya mutu daga kwanciya bacci a ɗakinsa dake Kubwa.
Wani mazaunin yankin ya ce lokacinsa ne ya yi, domin ya kwanta lafiya lau, da safiyar Lahadi aka tsinci gawarsa a daki.
Asali: Legit.ng