Wani dankareren Maciji ya tarwatsa dalibai mata a Hostel na wata Jami'a a Najeriya

Wani dankareren Maciji ya tarwatsa dalibai mata a Hostel na wata Jami'a a Najeriya

  • Dalibai mata na jami'ar Novena dake jihar Delta sun kidime da tsoro yayin da suka wayi gari da wata dankareriyar kasa a Hostel
  • Wata majiya ta bayyana cewa Daliban sun tashi da safe suka ga Macijin a kan gado kwance, tuni suka bar Hostel ɗin baki ɗaya
  • Hukumar jami'ar ta ce lamarin ba abin damuwa bane domin kowa yasan yankin na da wannan matsalar

Delta - Tsoro ya shiga zukatan ɗaliban jami'ar Novena, Ogume, ƙaramar hukumar Ndokwa ta yamma a jihar Delta, bayan wani dankareren maciji ya shiga Hostel ɗin su.

Wakilin jaridar Punch ya rahoto cewa an ga Macijin ne da safiyar ranar Litinin, kuma hakan ya saka tsoro da tashin hankali tsakanin ɗaliban Mata.

Wata majiya a jami'ar ta shaida mana cewa ɗaliban sun farka da misalin ƙarfe 5:30 na subahi, suka ci karo da macijin a kan gado.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An tsinci gawar mai haɗa wa Mataimakin shugaban ƙasa takalmi a Abuja

Novema University
Wani dankareren Maciji ya tarwatsa dalibai mata a Hostel na wata Jami'a a Najeriya Hoto: hotels.ng
Asali: UGC

Majiyar tace:

"Mun ga wani dankareren Maciji da ya kwana tare da mu a wuri ɗaya a ɗaya daga cikin Hostel ɗin mata. Macicin ya kutso cikin gidan kuma ya hau kan gado."
"Daya daga cikin ɗalibai mata da ta kwana a ɗakin ta tsorata ta yi ƙara, wanda hakan ya jawo hankalin yan uwanta ɗalibai. Yanzun da nake magana daliban sun bar gidan kwanan."

Wane mataki Jami'ar ta ɗauka?

Jami'in hulɗa da jama'a na jami'ar, Mista Emmanuel Odishika, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.

A kalamansa ya ce:

"Yankin suna da matsalar Macizai kuma lokaci zuwa lokaci ɗalibai kan tsinci kan su a irin wannan matsalar, amma Macizan ba su cutar da kowa."
"Jami'ar ta kai shekara 16 da kafuwa, tun shekarar 2005. Tun wancan lokacin macijin bai taɓa cutar da kowa ba. Ba shi da cutarwa."

Kara karanta wannan

Da-Dumi-Dumi: Lamari ya ɗau zafi, Ministan Buhari ya fice daga dakin taro da Daliban Najeriya

"Mun saba faɗa wa sabbin ɗaliban da muka ɗauka, tsofaffin ɗalibai ba su tsorata saboda sun san abinda ke faruwa. Ba zamu iya hana Macijin yawo ba."

A wani labarin na daban kuma Wani ma'aikacin jami'a ya mutu a cikin ruwan shakatawa a Hotel

Wani ma'aikaci a jami'ar UNICAL ya rasa rayuwarsa yayin da yaje Otal shan iska saboda zafin da ake a birnin Kalaba.

Wata majiya ta bayyana cewa da farko an nemi mutumin an rasa amma wajen karfe 2:00 na dare aka ga gawarsa a saman ruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262