Ana tsaka da yakin Rasha da Ukraine, Shugaba Buhari ya fice Najeriya, ya nufi Turai
- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai halarci taron zaman lafiya a Farisa, wanda aka shirya gudanarwa ranar 11 ga watan Maris
- Domin samun halartar taron na duniya, shugaban ƙasa ya bar fadarsa Aso Villa ranar 26 ga watan Fabrairu, 2022
- Buhari zai tattaunawa da shugabannin duniya kan abin da ya shafi zaman lafiya, tattalin arziki da lamarin Korona
A ranar 26 ga watan Fabrairu, 2022, shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya dira Faris, babban birnin kasar Faransa, domin fara ziyarar aiki ta mako biyu.
A rahoton da TVC News ta tattaro, Jirgin shugaba Buhari ya ɗira a filin sauka da tashin jiragen sama na Le Bourget da misalin ƙarfe 7:45 na daren ranar Asabar.
A cikin ziyarar mako biyu, Ana tsammanin shugaban ƙasan zai halarci taron zaman lafiya na kwana uku da aka shirya gudanarwa daga ranar Jumu'a 11 ga watan Maris, zuwa Lahadi 13 ga watan Maris.
Muhimman abubuwan da Buhari zai maida hankali
Shugaba Buhari zai tattauna kan dankon dangantakar Najeriya da Faransa da suka haɗa da, ƙara faɗaɗa alakar tattalin arziki, haɗa kai wajen samar da tsaro, Ilimi, Lafiya da magance barazanar COVID19 ga tattalin arzikin duniya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Haka nan, Buhari zai haɗu da shugabannin duniya da suka haɗa da shugabannin kungiyoyin duniya, yan kasuwa da sauransu domin tattauna hanyoyin zaman lafiya.
Ana sa ran shugaba Buhari zai yi jawabi a wurin taron, inda zai faɗa wa shugabannin halin ni 'ya su da Najeriya ta shiga da kokarin gwamnatinsa na dawo da zaman lafiya zuwa yau.
Sama da wakilai 110 daga sassan duniya, da suka haɗa da shugabannin ƙasashe 54 da gwamnati suka halarci taron na farko da aka gudanar a shekarar 2018.
Shugaban Rasha Vladimir Putin, Firaministan Ƙanada, Justin Trudeau da Nobel Laureate Nadia Murad na cikin waɗan da suka halarci taron a baya.
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta lallasa PDP, ta lashe zaben cike gurbi a jihohi biyu
Hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben maye gurbi da aka gudanar ranar Asabar a wasu mazabu na jihohin Ondo, Cross River.
Hukumar ta sanar da yan takarar APC a mazabun guda biyu, a matsayin wadan da suka lashe zabukan da yawan kuri'u.
Asali: Legit.ng