Gwamnatin jamhuriyyar Nijar ta saki kwamandojn Boko Haram daga Kurkuku

Gwamnatin jamhuriyyar Nijar ta saki kwamandojn Boko Haram daga Kurkuku

  • Don sulhu da zaman lafiya, Shugaban jamhuriyyar Nijar ya yafewa wasu yan ta'adda dake tsare a Kurkuku
  • Wannan shine karo na farko da gwamnatin kasar zata bayyana irin wannan mataki da samar da zaman lafiya
  • Wannan ya biyo bayan yafewa yan ta'addan Boko Haram da gwamnatin Najeriya ke yi tare da yunkurin canza musu tunani

Gwamnatin jamhuriyyar Nijar ta saki kwamandojn yan ta'adda cikin har da yan Boko Haram daga Kurkuku cikin sabon shirin sulhu da ake yi, kafafen yada labarai a kasan sun bayyana ranar Alhamis.

Shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum, ya yi wannan sanarwan ne ranar Juma'a yayin wata ganawar tsaro da manyan jami'an Soji da Sarakunan gargajiya suka halarta.

An ruwaito Bazoum da cewa:

"Na ga yan ta'adda tara. An bani shawaran na sakesu kuma na karbi bakuncinsu a fadar shugaban kasa saboda zaman lafiya nike so."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gobara ta sake kaca-kaca da sansanin yan gudun hijira a Borno

An tsare wadannan yan ta'adda ne a kurkukun Koutoukale dake kudancin garin Kollo, Bazoum ya kara.

Gwamnatin jamhuriyyar Nijar ta saki kwamandojn Boko Haram daga Kurkuku
Gwamnatin jamhuriyyar Nijar ta saki kwamandojn Boko Haram daga Kurkuku
Asali: Twitter

Wata majiya daga fadar shugaban kasar Nijar ta bayyana cewa wannan ne karo na farko da za'a bayyana labarin sakin yan ta'adda don sulhu a kasar, rahoton AFP.

Majiyar tace an fara sakin yan ta'addan ne cikin watanni uku da suka gabata.

Boko Haram Ta Kashe Ɗan Basarake Da Wasu 'Yan Gudun Hijira a Borno

A wani labarin, wasu da ake zargin mayakan Boko Haram/ISWAP ne sun kara kai hari kauyen Kautikari da ke karkashin karamar hukumar Chibok inda suka halaka dan dagacin kauyen, Bulama Wadir da wasu ‘yan gudun hijira biyu da ke garin, Vanguard ta ruwaito.

Babu nisa sosai tsakanin kauyen Kautikari da garin Chibok, kuma harin ya auku ne bayan wani kazamin farmaki da suka kai a watan Janairun 2022 wanda suka yi garkuwa da fiye da mutane 10 yawanci mata da yara.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

Sun banka wuta a coci mafi girma da ke makwabtaka da dajin Sambisa.

Farmakin yana kara yawaita a kauyen Kautikari, Pemi, Korohuma da sauran kauyaku da ke zagaye da Chibok tun watan Janairun wannan shekarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: