Shin na taba fadi zaben fidda gwani ne?, ina da tabbaci: Atiku ya yi alfahari
- Har yanzu, tsohon dan takaran kujeran Shugaban kasa bai bayyana niyyarsa na takara a zaben 2023
- Alhaji Atiku Abubakar kamar yadda yayi a 2019, ya kai ziyara ta musamman wajen tsohon maigidansa
- Ya yi jawabi a takaice wa manema labaran da suka bukaci jin ta bakinsa na zaben 2023
Abeokuta - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa tsofaffin yan siyasa basu hana matasan neman kujeran shugaban kasa a 2023 ba.
Ya yi watsi da maganar cewa tsaffin yan siyasa su hakura don matasa suyi takara a zaben badi.
Atiku ya bayyana hakan ne ranar Asabar a Abeokuta, jihar Ogun, bayan ganawa da tsohon shugaban kasa kuma maigidansa, Olusegun Obasanjo, rahoton Daily Trust.
Atiku ya ce nan ba da dadewa ba zai bayyana niyyar takararsa a zaben 2023.
Hakazalika ya bayyana cewa yana da tabbacin nasara a zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP.
Yace:
"Shin na taba fadi zaben fidda gwani ne? Ina da tabbaci,"
"Matasa suyi takara idan suna so. Takara ce. Demokradiyya ce."
Rahoton ya kara da cewa yanzu haka Atiku ya kai ziyarar ban girma wajen Sarkin kasar Egba, Oba Adedotun Gbadebo.
2023: Idan Baka Fito Takara Ba, Za Mu Ɗauke Ka Rago Kuma Matsoraci, Ƙungiya Ga Atiku
Matasan kudancin Najeriya sun huro wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wuta akan kin bayyana kudirinsa na takarar shugaban kasa a zaben 2023 da ke karatowa.
The Punch ta rahoto cewa matasan da ke karkashin kungiyar hadin kan matasan kudu, SOYA sun nemi ya fito fili ya bayyana kudirinsa ko kuma su fassara shirunsa a matsayin tsoro.
Shugaban SOYA, Ismail Ridwan, yayi wannan furucin a Abeokuta, Jihar Ogun a ranar Litinin yayin wani taro na manema labarai wanda ‘yan kungiyar na kudu maso yamma suka shirya don goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar.
Asali: Legit.ng