Matar aure ta sace kanta da kanta, ta karbi kudin fansa hannun wani saurayin Facebook,ta saya gida
- Wata matar aure kuma mai ciki ta shiga soyayya da wani mutumi mazaunin birnin tarayya Abuja ta shafin Facebook
- Bayan kwashe lokaci suna soyew ata hada baki da wani don amsa makudan kudade hannun mutumin
- Sun yi amfani da hanyar garkuwa da kanta kuma suka karbi kudin fansa ta naira milyan biyu
Wata matar aure mai juna biyu, Jamila Ardo, ta shiga hannun hukuma kan zargin laifin garkuwa da kanta kuma ta karbi kudin fansa hannun masoyinta na Facebook.
Jamila, wacce yar Wauru Jobe ne a karamar hukumar Yola ta kudu ta jihar Adanawa ta sace kanta kuma ta karbi fansan N2m hannun Mallam Ahmed Adamu, wani masoyinta dake Abuja.
Ana zargin matar da hada kai da wani mai suna Abdulaziz wajen garkuwa da kanta don damfarar wani mai sonta.
Matar Aure Mai Ciki Ta Yi Garkuwa Da Kanta, Ta Siya Gida Da Kuɗin Fansar Da Ta Karɓa Daga Hannun Masoyinta Na Facebook
Ance tayi amfani da kudin wajen sayen gida.
Matar da Adamu sun fara soyayya ne ta Facebook, amma bai san matar aure bace.
Jaridar Punch ta tattaro cewa duk da cewa basu taba haduwa ba, amma dare daya wani Abdulaziz ya kira masoyin yace masa an yi garkuwa da ita kuma an nemi kudin fansa.
Adamu cikin tausayi ya biya kudin fansan asusun banki mai suna, Amina Mohammed.
Rahoton yan sanda yace:
"Bayan karban kudin, ta fadawa Adamu cewa masu garkuwa da mutanen sun sake ta."
"A lokacin Adamu ya fara zargi kuma ya shigar da kara ofishin yan sanda ranar 16 ga Nuwamba, 2021."
Jami'an tsaro bayan bincike sun damke mai asusun bankin da aka tura kudin kuma aka bibiyeta aka damketa.
Daga baya aka gurfanar da ita gaban kotun majistare dake Yola kan laifin garkuwa da mutane.
Lauyan Jamila, C Crowealth ya bukaci kotu ta baiwa Jamila damar ganin Likiti saboda juna biyun da take dauke da shi.
Alkalin, Digil, ya bada belin kuma ya dage karar zuwa ranar 10 ga Maris, 2022, amma yace a garkame sauran.
Asali: Legit.ng