Bayan watanni 6, an gurfanar da wadanda ake zargi da hallaka yaron Sanata a gaban kotu
- Wadanda aka zargin da hannusu a mutuwar Abdulkarim Na’Allah za su yi shari’a da ‘yan sanda
- Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fitar da jawabi, ta ce ta maka wasu mutane uku a gaban Alkali
- Wadannan mutanen ne ake zargi da laifin kisa, biyu daga cikinsu ba su halarci zaman kotun ba
Kaduna - Wadanda ake tuhuma da laifin kisan yaron Bala Na’Allah watau Abdulkarim Na’Allah sun bayyana a gaban wata babban kotun jihar Kaduna.
Jaridar Punch ta rahoto cewa wadanda aka kama, kuma aka kai su gaban Alkali sun hada da Bashir Mohammed, Nasiru Balarabe da kuma Suleiman Salisu.
Rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna, ta fitar da jawabi na musamman ta na tabbatar da wannan.
Mai shari’a Amina Bello ce ta ke sauraron wannan kara, inda ake zargin wadannan mutane da laifin kisa, fashi da makami, da taimakawa wajen laifi.
A dakata tukuna - Alkali
Wani jami’in gwamnatin jihar Kaduna, Dr. Dari Bayero ya bukaci a dakata da wannan shari’a saboda wasu daga cikin wadanda ake zargin ba su je kotu ba.
Bugu da kari, wadannan mutane biyu ba su aiko da wakilin da zai tsaya masu a kotun ba. Bayero ya ce dole ne wanda ake yin shari’a da shi ya halarci kotu.
Emmanuel wanda ya tsayawa Suleiman Salisu ya shaida cewa wanda ya tsayawa a gaban kotu bai da isasshen lafiya, don haka ya ke neman bada belinsa.
An ki bada beli
Jaridar nan ta Tribune ta fitar da rahoto cewa Alkali bai yi na’am da rokon Avong Emmanuel ba, inda kotu ta ki bada belin daya daga cikin wadanda ake zargi.
Alkali ya daga wannan shari’a, ya ce a dawo ranar 21 ga watan Maris 2022 domin a gurfanar da wadannan mutane uku ta yadda za a fara yin shari’a da kyau.
Tun a watan Agustan 2021 ne ake zargin wadannan mutane uku sun dura gidan Abdulkarim Na’Allah a unguwar Malali a Kaduna, a karshe suka hallaka shi.
Okorocha ya shiga uku
Ku na da labari EFCC ta fara samun nasara a kan Rochas Anayo Okorocha, Alkali ya bukaci a karbe wani katafaren gidan da ya mallaka a kwaryar Abuja.
Hukumar EFCC ta na zargin cewa da kudin gwamnatin Imo aka saye gidan, don haka kotu ta ce a karbe wannan kadara da ke Garki, har sai sun karkare shari’a.
Asali: Legit.ng