Bazawara ta maka mahaifinta a kotu, ta ce karo na 3 kenan da yake mata auren dole

Bazawara ta maka mahaifinta a kotu, ta ce karo na 3 kenan da yake mata auren dole

  • Wata bazawara mai suna Sadiya mai shekaru 25 da haihuwa ta maka mahaifinta gaban wata kotun shari'ar Musulunci da ke Rigasa
  • Kamar yadda Sadiya ta sanarwa kotu, mahaifinta ya yi mata auren dole kuma wannan ne karo na uku, hakan yasa ta bar gidan shi
  • Mahaifin Sadiya, Malam Usman ya musanta hakan inda yace da kanta ta kawo wanda take so amma daga bisani tace bata son sa

Kaduna - Wata bazawara mai shekaru 25 mai suna Sadiya a ranar Laraba ta maka mahaifinta mai suna Malam Usman a gaban wata kotun shari'ar Musulunci da ke zama a Rigasa, Kaduna, kan zarginsa da take da yi mata auren dole.

Mai korafin wacce ke zama a yankin Rigasa da ke Kaduna, ta sanar da kotun cewa wannan shi ne aurenta karo na uku, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An Yi Ƙarar Wata Mata Saboda Lakaɗa Wa Maƙwabcinta Duka Bayan Ta Mallake Masa ‘Kitchen’

Bazawara ta maka mahaifinta a kotu, ta ce karo na 3 kenan da yake mata auren dole
Bazawara ta maka mahaifinta a kotu, ta ce karo na 3 kenan da yake mata auren dole. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: Facebook
"Mahaifina ne ya shirya tare da daura min auren dole ba tare da barin na san wanda zan aura ba tun farko. Aurena na farko, na biyu da na uku duka auren dole ne da mahaifina ya shirya.
"Ba zan cigaba da zama ba. Ina son wannan kotun da ta tsinke igiyoyin auren," tace.

Ta sanar da kotun cewa a halin yanzu ta na zama ne a yankin Unguwan Sarki da ke jihar.

Vanguard ta ruwaito cewa, a bangarensa, wanda ake karar ya ce diyarsa da kanta ta kawo masa mutumin gida amma daga baya tace bata son shi.

"Ikirarin da take yi na cewa bata san shi ba duk karya ne. Ban san inda diyata take zama ba yanzu. Ta bar gida a ranar aurenta. Ina rokon kotu da ta umarci diyata da ta dawo gida da gaggawa," yace.

Kara karanta wannan

Kotu ta garkame magidanci a gidan yari bayan ya kara aure babu sanin uwargidansa

Alkalin kotun, Malam Salisu Abubakar Tureta bai amsa bukatar wanda ake zargi ba amma ya umarci wacce ta yi kara da ta koma gidan hakimin Rigasa.

Ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar goma ga watan Maris domin mai korafin ta gabatar da shaidunta.

Ya matsa a bashi kasonsa: Matashi ya maka mahaifiyarsa a kotu kan gadon mahaifinsa, mutane sun magantu

A wani labarina daban, wani matashi ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan ya wallafa wani abu da abokinsa ya aikata.

A wata wallafa da OnyedikaAnambra ya yi a kafar sada zumunta ta zamani ya bayyana yadda mahaifin shakikin abokinsa ya rasu ya bar wa iyalansa dukiya.

Abokin nasa ya yanke shawarar maka mahaifiyarsa kotu akan dukiyar. Kamar yadda ya wallafa:

“Yanzu na samu labarin yadda wani shakikin abokina ya kai mahaifiyarsa kotu akan dukiyar da mahaifinsa ya mutu ya bari. Yaron ya na kokarin kanainaye dukiyar duk da mahaifiyarsa ta na da rai. Kada mu haifi dan banza fa a rayuwar nan.”

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU za ta yi zaman farko da Gwamnatin Tarayya mako 1 da fara yin yajin-aiki

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: