Yanzu-yanzu: Buhari ya dage rattafa hannu kan dokar zabe zuwa ranar Juma'a
- Buhari ya sanar da sabon ranar rattafa hannu kan sabuwar dokar zaben da za'ayi amfani a 2023
- Majalsar dokokin tarayya ta kwan biyu da mikawa Shugaba Buhari dokar da aka yiwa gyaran fuska
- Mai magana da yawun Buhari da farko yace za'a rattafa hannu ranar Laraba
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya dage rattafa hannu kan sabuwar dokar zaben Najeriya ranar Juma'a, 25 ga watan Febrairu, 2022.
ChannelsTV ta ruwaito majiya daga fadar shugaban kasa cewa da farko Buhari ya yi niyyar rattafa hannu yau Laraba, amma ya canza ra'ayinsa.
A cewar majiyar, wannan karon Shugaban kasan zai cika alkawarinsa.
A ranar Talata, an ce nan da yan awanni Shugaba Muhammadu Buhari zai rattafa hannu kan dokar zaben da aka yiwa gyaran fuska yayinda ake shirin shiga zaben 2023.
Mai magana da yawun Shugaban kasa, Mr Femi Adesina, ya bayyana hakan ranar Talata yayin hira a shirin Sunrise Daily na tashar ChannelsTV.
Ina goyon bayan Buhari kan kin sanya hannu a dokar zabe, Sanata Adamu
Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana a ranar Laraba, 29 ga watan Disamba, cewa ya yi farin ciki da ganin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai sanya hannu a gyararren dokar zabe ba.
Adamu ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya a Keffi cewa Majalisar dokokin bata da hurumin aiwatar da wani kudiri da zai yanke yadda jami’iyyu za su zabi yan takararsu.
Adamu ya ce ba bakon abu ne kuma rashin adalci ne a zo da wani doka da zai takaita yadda jam’iyyu za su gudanar da zabensu.
Yace yana goyon bayan shugaban kasa a kan kin saka hannu a kudirin.
Yac ya kamata mu yi godiya cewa kin saka hannun da Buhari yayi yana da amfani sosai. Shi mutum ne mai alkibla; mai zurfin tunani da tsare-tsare.
Asali: Legit.ng