Tuna baya: Abin da APC ta fada sa’ilin da ASUU ta yi dogon yajin-aiki a mulkin Jonathan

Tuna baya: Abin da APC ta fada sa’ilin da ASUU ta yi dogon yajin-aiki a mulkin Jonathan

  • Akwai lokacin da kungiyar malaman jami’a ta ASUU ta shiga wani dogon yajin-aiki a shekarar 2013
  • Tsakanin 2011 da 2015, Goodluck Jonathan ne yake kan mulki, Jam’iyyar APC kuma ta na adawa
  • APC ta fito tayi jawabi tana kiran gwamnatin tarayya ta cika alkawuran da tayi wa kungiyar ta ASUU

Legit.ng Hausa ta kakkabo wannan tsohuwar ajiya, yayin da a halin yanzu malaman kasar suka tafi wani yajin-aikin jan-kunne da za ayi makonni hudu.

Daily Post ta rahoto cewa Lai Mohammed ya fitar da wannan jawabi ne a watan Agustan 2013, kusan watanni hudu kafin kungiyar ta janye yajin-aikin.

A lokacin da APC ta goyi bayan ASUU, Alhaji Lai Mohammed shi ne sakataren yada labaran jam’iyyar. A yau shi ne ke kan kujerar Ministan labarai.

Ministan na yau ya zargi Gwamnatin PDP da rashin ba harkar ilmi muhimmancin da ya kamata, kuma ya caccaki Ministan ilmin lokacin, Nyesom Wike.

Kara karanta wannan

Kun mayar da lakcarori bayi: ASUU ta caccaki gwamnatin Buhari kan batun albashi

A jawabin da ya fitar a Abuja, Lai Mohammed ya ce Najeriya tana yin asarar $120m duk wata, amma ta ki biyan ASUU hakkinta da ta ke nema tun 2009.

A cika alkawari - APC

“ASUU ba wata sabuwar bukata ta kawo bayan yarjejeniyar da tayi da gwamnati a 2009 ba. Kyawun alkawari cikawa, saba alkawari yana biye da sakamako.”
Lai Mohammed
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

“Babu sasantawar da za ayi kan N87bn da ASUU ta ke nema a matsayin alawus din EAA. Wannan kudi ba komai ba ne kan N1tr da aka warewa ‘yan majalisa.”
“Ko idan aka kamanta kudin da abin da aka kashe yayin da Minista ya dauki jirgin sama domin nemo bashin Dala biliyan 1 a kasar Sin, dauke da alawus dinsa.”

Kara karanta wannan

Shiga yajin-aikin ASUU ke da wuya, Malaman FCE sun soma barazanar rufe makarantu

FG ta damu da ilmi kuwa?

“Hakan ya nuna inda gwamnatinmu ta ke maida hankali, tayi watsi da ilmi, ta ki cika alkawarin da aka yi tun 2009, amma ana kashe N3tr a tallafin man fetur.”
“Ana kashe N10bn duk shekara domin gyara jiragen dake fadar shugaban kasa, yayin da ba a yin komai a kan masu satar ganguna 400, 000 na mai a kullum.”

APC: Abin da ya dace ayi

“Abin da mu ke cewa, idan gwamnati ta rage facaka da dukiyar kasa, za a samu kudin da za a biya malamai, a inganta binciken ilmi, a samar masu da gine-gine.”
“Malaman da suke cikin yunwa ba za su iya koyarwa ko suyi bincike ba. Ba mu mamaki don jami’an gwamnati sun tura yaransu karatu zuwa kasashen waje.”

Minista zai zauna da ASUU

Dazu aka ji cewa shugabannin kungiyar malaman jami’a na kasa su na shirin haduwa da Ministan kwadago a yau Talata domin a tattauna kan yajin-aikin na su.

Kara karanta wannan

Mu ma nan ba da dadewa ba da yiwuwan mu shiga yajin aiki, Kungiyar Malaman Poly ASUP

Farfesa Emmanuel Osodeke ya tabbatar da cewa za su yi wani zama tare da Chris Ngige a Abuja. Ma'aikatar tarayya ta bayyana cewa za ayi wannan zaman ne da rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng