Rashin tsaro: Tsohon Shugaba Jonathan ya yi hasashen yadda zaben 2023 zai kasance
- Kungiyar ECOWAS ta yi wani taro na musamman a Legas inda Dr. Goodluck Jonathan ya yi jawabi
- Wakilan kasashe daga Ghana, Liberiya, Guinea Bissau, Cote D’Ivoire, Sanagal da Nijar, sun zo taron
- Goodluck Jonathan ya ce za ayi zaben 2023 hankali kwance ba tare da an samu rigimar komai ba
Lagos - Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya ce zaben 2023 zai zama mai inganci da nagarta, duk da barazanar da ake fuskanta a yau.
TVC ta ce Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya na ganin rikici ba zai barke a zaben da za ayi a shekarar badi ba, ko da cewa ana fama da rashin tsaro a wasu wurare.
Rahoton ya ce Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana wannan a wajen wani taron kwanaki biyu na karawa juna sani da kungiyar ECOWAS ta shirya a Legas.
Da yake bayani a ranar 21 ga watan Fubrairu, tsohon shugaban na Najeriya ya ce yana kyautata zaton hukumar INEC za ta shirya zabe mai kyau a Najeriya.
Abin da Jonathan ya fada
“Na yi imani zaben da za ayi a Najeriya za su zama masu nagarta. Za a yi, a gama. Daga shekarar 1999 da aka dawo mulkin farar hula, mun ga zabubbuka iri-iri.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Na shiga wasu daga cikin wadannan zabe da aka yi, kuma kun san wannan da kyau.”
“Idan zabe ya zo, a kan shiga dar-dar cewa kasar nan za ta wargaje, amma ku na gani har yanzu ta na nan daram.”
“A lokacin da na ke mulki, na samu labarin cewa wasu sun rika dauke iyalinsu daga Najeriya (idan zabe ya zo), amma kuma babu wani abin da ya faru.”
“Saboda haka za a zo ayi zaben shekarar 2023, kuma kasar nan za ta zauna kalau yadda ta ke.”
- Goodluck Jonathan
An kafa majalisar COW
Daga jawabin da ya yi, jaridar Vanguard ta rahoto Jonathan yana bayani game da majalisar COW da kungiyar ECOWAS ta samar domin a tabbatar da zaman lafiya.
Dr. Jonathan ya ce an damkawa wannan majalisa ta dattawa nauyin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali ta hanyar lalama a yankin yammacin Afrika.
Ta'adin 'yan bindiga
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ya bayyana yadda aka samu saukin rashin tsaro bayan 'yan bindiga sun addabi mutane da sata da garkuwa da mutane.
An ji Lai Mohammed ya ce ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda, ya taimakawa jami'an tsaro wajen rugurguza masu kokarin tada kayar baya a fadin kasar nan.
Asali: Legit.ng