Lai Mohammed: Lakani 1 da Gwamnati ta yi amfani da shi aka samu saukin ‘yan bindiga
- Ministan yada labarai da al’adu Lai Mohammed ya bayyana yadda aka samu saukin rashin tsaro
- Lai Mohammed ya ce ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda, ya taimakawa gwamnati
- A cewarsa wannan ne ya ba jami’an tsaro damar ganin bayan ‘yan bindiga ba tare da wani kaidi ba
Abuja - Ayyana ‘yan bindiga da gwamnatin tarayya ta yi a matsayin ‘yan ta’adda, ya taimaka wajen inganta tsaro. Lai Mohammed ne ya bayyana wannan.
Rahoton da aka fitar a ranar 22 ga watan Fubrairu 2022 ya bayyana cewa Lai Mohammed ya yi wannan bayani da ya ziyarci ofishin Media Trust Ltd a Abuja.
Ministan yada labarai da al’adun kasar ya ce ayyanawar ta taimaka wajen bada damar amfani da karfi wajen murkushe masu kokarin tada kayar baya a Najeriya.
A cewarsa, a baya hakan ba zai yiwu ba, sai da gwamnatin tarayya ta dauki wannan matakin. Jaridar ta ce yanzu ana iya yakar 'yan bindiga da kowane makami.
Amfanin matakin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauka shi ne sojoji da ‘yan sanda za su iya ragargazar ‘yan bindiga a yanzu ba tare da kaukautawa ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jawabin Lai Mohammed
“Da ake surutu, na ce babu bambanci a sunan da aka kira su. Ina tunanin idan an kira su ‘yan ta’adda, zai ba sojoji da jami’an tsaro karin karfin rugurguza su.”
"Kamar idan ‘dalibai su na zanga-zanga ne, dole ayi amfani da harsashin roba da makamantarsu.”
“Idan aka cigaba da kiransu ‘yan fashin daji, za a samu togaciya da taka burki daga ‘yan sanda da sojoji, amma da aka kira su da ‘yan ta’adda, babu wani kaidi.”
Sojojin sama sun samu dama
“Ina tunanin wannan ya taimaka kwarai da gaske. Har wasu kayan aikin da sojojin sama suka saya ba za su yi aiki a kan ‘yan fashin jeji ba, sai ‘yan ta’adda.”
“Yanzu da aka ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda, za su iya amfani da makaman a kansu. Wannan ya sa aka ga ana samun cigaba a yakin da ake yi da su.”
An lalata da dalibai
Ku na da labari cewa watanni takwas da dauke dalibai 80 daga makarantar sakandaren gwamnatin tarayya da ke Yauri, jihar Kebbi, har yanzu wasu na tsare.
Duk da an biya kudin fansa ko an saki wasu ‘yan bindiga da ke tsare a gidan yari domin a fito da daliban, har yanzu shiru. Har ma 'yan bindiga sun yi wa wasunsu ciki.
Asali: Legit.ng