Da duminsa: Shugaba Buhari ya dawo gida daga Brussels, Belgika

Da duminsa: Shugaba Buhari ya dawo gida daga Brussels, Belgika

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan kwanaki hudu a nahiyar Turai
  • Buhari ya wakilci Najeriya a birnin Brussels inda aka yi taron hadin kai tsakann kasashen Turai da Afrika
  • Tun kafin ya dawo, shugaba Buhari ya amsa goron gayyatar kai ziyara kasar Czech

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari dawo gida Najeriya bayan tafiyarsa zuwa Belgium inda ya hallarci taron hadin kai na gamayyar kasashen Turai da gammayar kasashen Afrika karo na shida.

Hadimin Shugaba Muhammadu Buhari na yaa labarai gidajen rediyo da talabijin, Buhari Sallau, ne ya sanar da labarin tafiyarsa a shafinsa na Facebook.

Shugaba Buhari
Da duminsa: Shugaba Buhari ya dawo gida daga Brussels, Belgika Hoto: Buhari Salau
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Muna hanyar zuwa Kebbi daurin aure aka ce yan bindiga sun tare hanya, Shehu Sani

Sallau, a cikin rubutun da ya wallafa a da yammacin nan ya ce:

"Shugaba Muhammadu Buhari ya koma Abuja bayan nasarar halartan taron hadin kasashen Afrika da na Turai a Brussels, ."

Shugaba Buhari ya amsa goron gayyata zuwa jamhuriyar Czech

Shugaba Muhammadu Buhari ya amsa goron gayyatar da shugaban kasar jamhuriyyar Czech, Milos Zeman, na ziyartar kasar Turan a wannan shekara ta 2022.

Wannan ya faru ne a zaman diflomasiyyar da ya gudana tsakanin Buhari da Milos Zeman ranar Alhamis a Brussels, kasar Beljika.

A zaman, shugabannin kasashen biyu sun amince a karfafa zumunta tsakaninsu.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, a jawabin da ya saki ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng