Wajibi ne a bamu shugabancin kasa ko kuma mu bar Najeriya, Dattawan Igbo

Wajibi ne a bamu shugabancin kasa ko kuma mu bar Najeriya, Dattawan Igbo

  • Dattawan Igbo na barazanar ballewar yankin daga Najeriya idan ba'a basu shugabancin kasar nan ba a 2023
  • Manyan masu fada a jin kabilar sun lashi takobin hukunta duk dan siyasar Igbo da ya karbi kujeran mataimakin shugaban kasa
  • A cewarsu, kawai a baiwa dan kabilar shugabancin Najeriya don ya gyara kasar

Sannanu kuma masu fada a ji na kabilar Igbo, karkashin kungiyar dattawan kabilar Igbo IECF, sun bayyana cewa wajibi ne a baiwa yankin kujeran shugaban kasar Najeriya a 2023.

Hakazalika sun gargadi yan siyasar yankin kada wanda ya kuskura ya yarda a daukeshi matsayin dan takarar kujeran mataimakin shugaban kasa.

Shugaban kungiyar wanda yake tsohon gwamnan jihar Anambra, Chief Chukwuemeka Ezeife, ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai ranar Laraba a Abuja, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

IBB ga 'yan siyasa: Kar ku yi wasa da hadin kan 'yan Najeriya

Dattawan Igbo
Wajibi ne a bamu shugabancin kasa ko kuma mu bar Najeriya, Dattawan Igbo
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Eziefe ya jaddada cewa ko dai a baiwa Igbo shugaban kasa ko kuma yankin ta balle daga Najeriya.

Yace:

"Bisa kira ga jama'a suke yi a baiwa kudu shugabancin kasa a 2023, kungiyar dattawan Igbo na kira ga yan siyasan yankin kudu maso gabas su bayyana niyyar takararsu wa kujerar shugaban kasa kuma suyi da gaske."
"Da gaske muke. Kada ku saurari masu neman kujerar abokin tafiya, saboda Igbo ba zata yarda wani 'danmu ko 'yarmu ta karbi kujeran mataimakin shugaban kasa ba a 2023."
"Ko dai a bamu kujeran shugaban kasa a 2023 don mu canza lalaci, talauci, rashin tsaro, rashawa da rashin iya mulki dake Najeriya ko kuma mu fita."

Wadanda ke halarce a taron sun hada da tsohon Ministan Ilmi, Farfesa S. C Madubuike; Sakataren janar na Ohazaeze Ndgibo (Abuja), Dr Nkonye Kingsley; dss.

Kara karanta wannan

2023: Wata Ƙungiya Ta Sake Shawartar Atiku Ya Haƙura Da Batun Sake Fitowa Takarar Shugaban Ƙasa

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng