Mutum daya ya mutu, yayin da yan bindiga suka yi awon gaba da ɗan Basarake a Abuja

Mutum daya ya mutu, yayin da yan bindiga suka yi awon gaba da ɗan Basarake a Abuja

  • Wasu tawagar masu garkuwa da mutane sun tare ɗan Basaraken ƙauyen Gwombe a Abuja, sun yi awon gaba da shi
  • Rahoton da muka samu ya nuna cewa maharan sun bindige direban ɗan basaraken har Lahira yayin da ya yi yunkurin guduwa
  • Har zuwa yanzun hukumar yan sandan babban birnin tarayya Abuja ba tace komai ba game da lamarin

Abuja - Yan bindiga sun sace Junaidu Danjuma, ɗan Basaraken yankin Gwombe, Gwargwada, karamar hukumar Kuje a birnin Abuja, Mai Martaba Danjuma Magaji Jangaba.

Daily Trust ta tattaro cewa Direban dake ɗauke ɗan Basaraken a cikin Mota, Kabiru Sani, ya rasa rayuwarsa yayin da ya yi yunkirin tsere wa.

Yan bindiga
Mutum daya ya mutu, yayin da yan bindiga suka yi awon gaba da ɗan Basarake a Abuja Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wani mazaunin Gwembe, mai suna Salihu, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 5:23 na yamma, lokacin da yan ta'addan ɗauke da muggan makamai suka tare hanyar Gwargwada-Gwombe.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wuta ta kama a dakin kwanan Dalibai suna tsaka da bacci, ta yi mummunan barna

Yace ɗan Sarkin na kan hanyar komawa gida daga wani kauye dake kusa da Rubochi a cikin Mota, lokacin da yan garkuwan suka tare hanya ba zato ba tsammani.

The Nation ta rahoto Mutumin ya ce:

"Yayin da yaga masu garkuwa ne mutumin dake ɗauke da ɗan Basaraken ya yi yunkurin tsere wa, yan bindigan suka buɗe masa wuta ya mutu nan take suka yi gaba da ɗan Basaraken."

Shin Masarauta ta san abin da ya faru?

Sarkin Gwargwada-Ugbada, mai martaba Alhaji Hussein Agabi Mam (HRH), ya tabbatar da sace ɗan magajin garin Gwombe a wata fira ta wayar Salula.

Kakakin rundunar yan sanda reshen babban birnin tarayya, DSP Adeh Josephine, ba ta ɗaga kiran wayan da aka mata ba, kuma ba ta turo amsoshin sakon da aka tura mata ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Duk a babi daya muke, Dattawan Arewa sun gana da Obasanjo

A wani labarin na daban kuma Matar Aure ta maka mijinta a Kotu saboda ya ƙi amincewa sun yi aure

Wata mata ta gurfanar da wani mutumi a gaban kotu kan yaƙi amincewa an ɗaura musu aure da jimawa a jihar Kaduna.

Mijin yace ya na da alaƙa da matar amma ta bariki, amma ba su kai ga auren juna ba kamar yadda ta yi ikirari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262