Sanatoci sun kinkimo maganar binciken kwangilar N400bn da Obasanjo ya bada tun 2006
- Majalisar Dattawan Najeriya za ta binciki wata kwangilar gina dakunan shan magani da aka bada
- Tun a shekarar 2006 Gwamnatin Olusegun Obasanjo ta fitar da biliyoyin kudi domin ayi wannan aiki
- An ba wasu Sanatoci makonni shida su je su yi bincike domin a gano inda aka tsaya a kwangilar
Abuja - Majalisar dattawa ta bukaci a fara binciken wasu kwangilolin kiwon lafiya da suka ci Naira biliyan 400 a lokacin gwamnatin Olusegun Obasanjo.
The Guardian ta ce ‘yan majalisa sun dauko wannan aiki ne bayan kusan shekaru 15 da saukar Cif Olusegun Obasanjo, wanda ya bar mulki tun a Mayun 2007.
A wani rahoto da aka fitar a ranar Laraba, an ji cewa shugaban kwamitin kiwon lafiya a majalisar dattawa, Sanata Ibrahim Oloriegbe ya bijiro da wannan batu.
Majalisar dattawan kasar ta karbi shawarar Sanata Ibrahim Oloriegbe, ta bukaci kwamitocin ayyuka, gidaje da kuma na kiwon lafiya su gudanar da bincike.
Jaridar The Sun ta ce an bada umarni kwamitocin su kammala wannan bincike cikin makonni shida.
Dalilin wannan bincike
Majalisar ta ce ya zama dole a bankado wannan aiki ne saboda a lokacin an ware duka kudin kwangilar a wani babban banki, wanda yanzu ya ruguje.
A cewar Sanatocin, binciken zai taimaka wajen duba inda aka kwana wajen gina dakunan shan magani a kowace karamar hukuma da ke fadin kasar nan.
Kwangilar N400bn
An dauko wannan kwangilar a shekarar 2006 ne domin a gina dakin shan magani mai cin gadaje 60 a kananan hukumomi 774 da ake da su, shekaru 16 kenan.
Domin a aiwatar da wannan aikin, gwamnatin tarayya ta rika cire kudi daga asusun rarar mai na ECA da kuma asusun ajiyar kudin duka kananan hukumomi.
Ba wannan ne karon farko da aka ji majalisar tarayya ta na binciken gwamnatin Olusegun Obasanjo ba wanda ya yi mulki tsakanin shekarar 1999 da 2007.
Gwamnoni sun kai FG kotu
Ku na da labarin cewa Kayode Fayemi ya fadi dalilinsu na shiga kotun Allah ya isa da Gwamnatin tarayya domin raba masu gardama a kan dokar nan ta E.O 10.
Shugaban NGF ya zargi wasu Mukarrabai da ba Muhammadu Buhari gurguwar shawarar da ta sabawa dokar kasa, don haka aka raba masu gardamar a kotu.
Asali: Legit.ng