An yanka ta tashi: Kungiya za ta yi shari’a da Buhari da Ministansa a kotu, ta kinkimo Lauyoyi
- Socio-Economic Rights and Accountability Project ta shigar da karar Muhammadu Buhari a kotu
- Kungiyar ta bukaci sanin yarjejeniyar da aka cin ma kafin a kyale Twitter ta cigaba da aiki a Najeriya
- SERAP ta je kotu ne bayan samun takardar yarjejeniyar daga hannun Ministan labarai ya gagara
Lagos – Kungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project ta na karar shugaba Muhammadu Buhari a kan yarjejeniyarsa da kamfanin Twitter.
This Day ta ce kungiyar SERAP mai kokarin kare hakkin jama’a a Najeriya ta bukaci gwamnati ta fito da sharudan da ta ba Twitter kafin a ba su damar dawo aiki.
Ministan yada labarai da al’adu na kasa, Alhaji Lai Mohammed yana cikin wadanda aka cusa a shari’ar.
An shigar da wannan kara mai lamba FHC/L/CS/238/2022 a gaban babban kotun tarayya da ke Legas ne a ranar Juma’ar da ta wuce, 11 ga watan Fubrairu 2022.
SERAP ta na so Alkali ya tursasawa Muhammadu Buhari da Lai Mohammed fito da yarjejeniya da sharudan da gwamnatin tarayya ta cin ma da kamfanin Twitter.
Dalilin kai kara a kotu
A wannan kara da kungiyar mai zaman kanta ta kai a kotun da ke garin Legas, ta ce sanin dalla-dallar yarjejeniyar zai ba ‘Yan Najeriya damar su tofa albarkacinsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton ya ce kungiyar ta na zargin cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta amincewa Twitter su dawo aiki ne da sharadin za ta toshe hakkin mutane na magana.
Kafin a kai ga zuwa kotu, kungiyar SERAP ta aikawa Ministan labaran bukatar FOI, ta na mai neman samun takardar yarjejeniyar gwamnatin Najeriya da kamfanin.
Sai dai martanin da kungiyar ta samu daga ofishin Ministan kasar bai gamsar da ita ba. Abin da Lai ya ce kurum shi ne za a iya samun yarjejeniyar a kan yanar gizo.
An dauki Lauyoyi
Hakan ta sa aka samu lauyoyi biyu; Kolawole Oluwadare da Opeyemi Owolabi da suka yi karar Mai girma shugaban kasa da Ministan tarayyar a madadin kungiyar.
Yayin da lauyoyin suka dogara da sashe na 39 na kundin tsarin mulki da dokokin kare hakkin Bil Adama na Afrika, har yanzu ba a sa ranar da za a soma yin shari’a ba.
Mutuwar Magajin Gari
An ji cewa Muhammadu Buhari ya yi addu’a da alhini ga iyali, gwamnati da kuma mutanen jihar Sokoto a game da rasuwar Magajin Garin Sokoto, Alhaji Hasan Danbaba.
Shugaban kasa Buhari ya tura Abubakar Malami, Suleiman Adamu, Hadi Sirika da Muhammadu Maigari Dingyadi su je jihar Sokoto domin su yi ta’aziyya a madadinsa.
Asali: Legit.ng