Za a kara laftawa Gwamnatin Buhari ciwon kai, Kungiyar NUPENG na shirin yajin-aiki
- Kungiyar NUPENG ta zargi ma’aikatar ayyuka da gidaje da kokarin sace N621bn na gyara hanyoyi
- Shugabannin NUPENG sun fitar da jawabi, suka ce muddin aka taba wannan kudi, za a shiga yajin-aiki
- Ana zargin jami’an gwamnati da karkatar da wadannan kudi wajen kwangilolin da an cinye kudinsu
Abuja - A ranar Lahadi, 13 ga watan Fubrairu 2022, kungiyar NUPENG ta ma’aikatan man fetur da gas a Najeriya ta nuna goyon bayanta a kan tafiya yajin aiki.
Rahoton Vanguard ya bayyana cewa kungiyar NUPENG ta na goyon bayan direbobin tankokin mai su tafi yajin-aiki domin nunawa gwamnati rashin jin dadinsu.
NUPENG ta na ikirarin cewa bincike ya nuna mata jami’an ma’aikatar ayyuka da gidaje na tarayya sun karkatar da Naira biliyan 621 da aka ware na aikin titi.
A cewar kungiyar ta NUPENG, an wawuri wadannan kudin gyaran hanya. Tuni dai ma’aikatar tarayya ta karyata wannan zargi, ta ce sam ba hakan abin yake ba.
NUPENG tayi jawabi
Kungiyar ta fitar da jawabi ne ta bakin shugabanta da kuma sakatarenta na kasa, watau Williams Akporeha da kuma Olawale Afolabi a karshen makon da ya gabata.
Williams Akporeha da Olawale Afolabi sun ce gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa-da-tsaki na neman saba alkawarin da aka cin ma a zaman da aka yi a baya ba.
A karshen taron da kungiyar NUPENG tayi, an ci ma yarjejeniya cewa NNPC za ta fitar da Naira biliyan 621 domin gyara wasu rubabbun hanyoyi 21 a fadin Najeriya.
Jawabin ya ce a dalilin wannan ne kungiyar ta hakura da yajin-aiki. Don haka shugabannin NUPENG suka ce idan suka ji shiru, za su yi abin da suka yi niyyar.
Akporeha da Afolabi sun ce su na samun bayanai daga majiya mai karfi cewa gwamnonin jihohi da wasu jami’an ma’aikatar ayyuka da ‘yan siyasa na neman kawo cikas.
Shugabannin na NUPENG suka ce wadannan mutane sun fara taba kudin da aka ware, su na karkatar da wasu wajen ayyukan da tuni an fitar da kudin kwangilarsu.
The Guardian ta ce kamfanin NNPC za ta kashe wadannan makudan kudi har fiye da Naira biliyan 600 domin a gyara wasu titunan tarayyan da suka sukurkuce.
Badakala a NNPC
Kwanaki kun ji cewa kungiyar gwamnonin jihohin tarayya ta NGF ta fito ta jefi NNPC da zargi. Hakan na zuwa ne a lokacin da ake magana kan janye tallafin mai.
Gwamnonin na Najeriya su na tuhumar kamfanin mai na kasa, watau National Petroleum Corporation Limited (NNPC) da laifin sata da kin bayyana shirinsu.
Asali: Legit.ng