Sama da yan Boko Haram/ISWAP 30,000 sun mika wuya, Gwamna Zulum
1 - tsawon mintuna
Abuja - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa gwamnati ta samu yan ta'addan Boko Haram da ISWAP 30,000 da suka mika wuya daga Satumba 2021 kawo yanzu.
Gwamnan ya kara da cewa ba wai suna mika wuya don wani alkawarin kudi ko dukiya bane, suna yi don kansu ne.
Zulum ya tabbatar da cewa nan da lokacin zaben 2023 rikicin Boko Haram zata zo karshe a Najeriya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ga manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da shugaba Buhari.
Yace:
"Mika wuyan da yan Boko Haram ke yi ya dau sabon salo yanzu saboda yan ta'addan ISWAP sun fara saduda."
Kawo yanzu, mun samu akalla yan ta'addan Boko Haram da ISWAP 30,000 daga farko har yanzu. Mun fara samun yan ISWAP yanzu, amma yan Boko Haram sun fi yawa."
"A yadda abubuwa ke gudana... Boko Haram zai kare nan ba da dadewa ba."
Yayinda aka tambayesa shin rikicin zai kare nan da karewar wa'adinsa na farko a 2023, Gwamnan yace:
"Insha Allah. Ko yanzu a Borno mun samu sauki."
Asali: Legit.ng
Tags: