Hukumar Hisbah ta rusa kwalaben giya kimanin milyan hudu a Kano

Hukumar Hisbah ta rusa kwalaben giya kimanin milyan hudu a Kano

Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta lalata kwalaben giya sama da 3.8 million da aka damke yan watannin da suka gabata.

Kwamandan hukumar Hisbah, Harun Ibn-Sina, ya bayyana hakan yayin taro fasa kwalaben giya a Tudun Kalebawa, dake karamar hukumar Dawakin Tofa ranar Laraba, rahoton Vanguard.

Ibn-Sina ya yi bayanin cewa hukumar na samun nasarori wajen yaki da muggan kwayoyi da kayan maye sakamakon goyon bayan da gwamnatin jihar ke basu.

Yace:

"Wannan ne ya bamu daman samun umurnin kotun Majistare na fasa dukkan kwalaben giyan da ke hannunmu."
"Haramun ne sayar da giya, da shan giya da kayan maye."

Ya jinjinawa gwamnatin jihar Kano bisa kokarin da take yi wajen dakile ayyukan alfasha.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnati Ta Rufe Ofishin Hukumar Lantarki Saboda Yanke Wutar Ofishin Gwamna

Hukumar Hisbah ta rusa kwalaben giya kimanin milyan hudu a Kano
Hukumar Hisbah ta rusa kwalaben giya kimanin milyan hudu a Kano
Asali: UGC

Hakazalika, Gwamna Abdullahi Ganduje ya jaddada cewa gwamnatin jihar zata inganta albashin ma'aikatan Hisbah.

Ganduje, ya samu wakilcin dan majalisa mai wakiltar Albasu, Sunusi Usman-Batayya.

Ganduje yace Kan na daya daga cikin jihohi mafi zaman lafiya bisa kokarin gwamnatin jihar da masu ruwa da tsaki.

Gwamnan ya yi yiwa da al'ummar jihar su baiwa gwamnati goyon baya wajen inganta tarbiyyan matasa.

Yace:

"Kano ce jiha ta farko da ta kafa ma'aikatan harkokin addini a kasar nan."
"Hukuma Hisbah ta cigaba da aikinta saboda batagari sun samo sabuwar hanyar shigo da muggan kwayoyi jihar."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: