Hanifa Abubakar: Uwar gidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta kai ziyara Kano, tace wajibi a yi adalci
- Uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari ta kai ziyarar ta'aziyyar rasuwar Sheikh Ahmad Bamba da Hanifa Abubakar
- Aisha Buhari ta yi bayani mai ratsa zuciya game da Hanifa, inda tace ita ma uwa ce kuma tana da jikoki a makarantar Firamare
- Gwamna Abdullahi Ganduje ya tabbatarwa matar shugaban ƙasa cewa gwamnatinsa za ta tabbatar an yi adalci
Kano - Uwar gidan shugaban ƙasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta kai ziyara jihar Kano domin jajantawa gwamnati da al'umma bisa kisan Hanifa Abubakar da rasuwar fitaccen Malami, Dakta Ahmad Bamba.
A wani taron manema labarai da ta yi a gidan gwamnati, Aisha tace ta kawo ziyara ne a ƙashin kanta domin ta yi ta'aziyya ga iyalan mutanen biyu, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Aisha ta ce:
"Na zo nan jihar ne a karan kaina domin jajantawa gwamnan jihar Kano da matarsa, Sarkin Kano da kuma sauran mazauna jihar bisa rashin fitaccen malami, Sheikh Ahmad Bamba da Hanifa Abubakar."
"Muna addu'a kuma muna fatan za'a yi mata adalci. A matsayina na uwa ina da 'ya'ya da jikoki dake karatun Firamare yanzu haka, sun yarda da malaman su, muma iyaye mun amince da su."
"Dan haka idan har yara ba zasu samu kwanciyar hankali a makarantun su ba, hakan na nufin cewa al'umma ta canza zuwa wani abu daban. Ina ganin ya dace a ɗauki mataki dan kare makamancin haka nan gaba."
Tabbas za'a yi wa Hanifa Adalci - Ganduje
Da yake jawabin godiya, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar wa uwar gidan shugaban ƙasa cewa gaskiya zata yi halinta.
"Hanifa ɗiyar mu ce kuma ɗiyar kowane ɗan Najeriya ce. Mun damu sosai kuma mun ji daɗin wannan ziyara tun daga Abuja."
"Hatta lokacin da lamarin ya faru kin fito fili kin yi magana cewa kina fatan gwamnati zata ɗauki matakan tabbatar da an hukunta waɗan da suka aikata haka."
A wani labarin kuma Gwamnatin kasa ta haramtawa ma'aikata rungumar juna, Sunbata da kalaman batsa a wurin aiki
Kasar Mexico ta hana ma'aikatan dake karkashinta aikata wani abu da ya shafi Jima'i kamar rungumar juna da sumbatar juna a wurin aiki.
Wannan na kunshe ne a wasu sabbin dokokin da gwamnati ta fitar a hukumance ranar Talata, 8 ga watan Fabarairu 2022.
Asali: Legit.ng