Babban Alkalin Najeriya ya fadi ainihin abin da ya sa Gwamnati ba ta iya kama Barayi

Babban Alkalin Najeriya ya fadi ainihin abin da ya sa Gwamnati ba ta iya kama Barayi

  • Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN ya zargi Alkalai da kotu da kawo matsala wajen shari’o’i
  • Alkalin Alkalai na kasa, Tanko Muhammad ya ce bai dace Abubakar Malami ya ga laifin kotu ba
  • Mai shari’a Tanko Muhammad ya zargi gwamnati da dauko binciken da ya fi karfinta, ta kawo kotu

FCT, Abuja - Alkalin Alkalan Najeriya, Mai shari’a Tanko Muhammad ya maida martani ga babban lauyan gwamnati kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami.

Hakan na zuwa ne bayan an ji AGF Abubakar Malami SAN yana cewa bangaren shari’a ne ya kamata a gani da laifi a jinkirin da ake samu a manyan shari’o’i.

Da yake bayani a gidan talabijin, Daily Trust ta ce Abubakar Malami ya daura laifi a kan kotu, ya ce su suke kawo nawa a binciken rashin gaskiyar da ake yi a kasar.

Kara karanta wannan

Wanda ICPC ta ke zargi da laifin satar Naira miliyan 900 yana so ayi sulhu a wajen kotu

Isah Ahuruaka ya fitar da jawabi

Mai magana da yawun Mai shari’a CJN, Isah Ahuruaka ya maidawa Ministan martani inda ya ce ba kotu ya kamata a daurawa laifi ba, sai dai gwamnatin tarayya.

“A dokar kasa, bangaren shari’a bai da wani sashe na binciken masu laifi ko bankado marasa gaskiya, haka zalika bai da dakarun da za su tabbatar da hukuncin da ya zartar.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Amma mafi yawan lokuta, sashen bincike na gwamnatin tarayya kan shigar da karar da ba za su iya kare ta ko gabatar da shaidu a kotu ba, sai a gaza kama wanda ake zargi.”

- Isah Ahuruaka

Babban Alkalin Najeriya
Babban Alkalin Najeriya da Ministan shari'a Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Inda matsalolin su ke - CJN

Tanko Muhammad ya kara da cewa dokar ACJA ta na cikin abubuwan da ke kawo tasgaro, baya ga yawan shari’o’i da ake da su a gaban Alkalan da ba su da yawa.

Kara karanta wannan

Mutum 5 da suka ki karbar kujerun da Shugaban kasa Buhari ya ba su a Gwamnatinsa

Bugu da kari CJN Muhammad ya ce kotu na fama da karancin kayan aiki ko kayan aikin zamanin da. Gidan talabijin Channels TV sun fitar da wannan rahoto.

Akwai karancin kudi

A gefe guda, gwamnatin tarayya na zargin bangaren shari’an da rashin fitowa fili su bayyana abin da suke kashewa a kasafin kudi, don haka ake karancin rashin kudi.

Isah Ahuruaka da yawun babban Alkalin kasar ya musanya wannan zargi, ya ce su na gabatar da duk rokon kudin da suke bukata kamar yadda gwamnati ta ke tanada.

Tun daga kudin ayyuka, kudin kashewa, da muhimman abubuwa, CJN ya ce suna bayanin komai.

Takarar shugaban kasa

Daniel Bwala yana ganin tun da Bola Tinubu ya nuna sha’awar takara, hankali ma zai fada maka cewa ba daidai ba ne Yemi Osinbajo ya fito ya yi takara tare da shi a APC.

An ji Bwala ya na bada shawara cewa tun da Farfesa Osinbajo ba zai yi takara a zaben 2023 ba, sai ya fadawa mabiyansa su bi bayan tsohon mai gidansa watau Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng