An samu ci gaba: Majalisa ta amince a kara yawan makarantun lauyoyi a kasar nan
- Majalisar dattajai a Najeriya ta amince a sake kafa wasu cibiyoyi na ilimin lauya a fadin kasar nan
- Majalisar ta amince da kafa makarantun a shiyyoyi shida na kasar nan kamar yadda rahotanni suka bayyana
- A baya kasar na da makamantun lauyoyi shida, yanzu an samu karin bakwai bayan amincewar majalisar
FCT, Abuja - Majalisar dattijai a ranar Talata 8 ga watan Fabrairu ta zartas da wani kudiri na kafa karin makarantun lauyoyi a shiyyoyin kasar nan shida, Daily Trust ta ruwaito.
Hakan ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin shari’a, ‘yancin dan Adam da kuma harkokin doka, wanda Sanata Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti) ya jagoranta.
Jerin Makarantun Lauyoyi da ake dasu
Rahoton The Nation ya kawo adadin makarantun da ake dasu kafin a amince da karin. Makarantun lauyoyi da ake da su a yanzu sune kamar haka:
- Legas (Kudu maso Yamma)
- Abuja (Arewa ta Tsakiya)
- Yola (Arewa maso Gabas)
- Kano (Arewa maso Yamma)
- Enugu (Kudu maso Gabas)
- Yenegoa (Kudu maso Kudu)
Karin makarantu 7 da za a kafa
Karin cibiyoyin da majalisar ta amince da su sun hada da:
- Makarantar Lauyoyi ta Kogi (Arewa ta Tsakiya)
- Makarantar Lauyoyi ta Maiduguri, Borno (Arewa maso Gabas)
- Makarantar Lauyoyi ta Argungu, Kebbi (Arewa maso Yamma)
- Makarantar Lauyoyi ta Okija, Anambra (Kudu maso Gabas)
- Makarantar Lauyoyi ta Orogun, Delta (Kudu maso Kudu)
- Makarantar Lauyoyi ta Ilawe, Ekiti (Kudu maso Yamma)
- Makarantar Lauyoyi ta Jos, Filato (Arewa Ta Tsakiya)
Majalisa ta tabbatar da Farfesa Ayo Omotayo a matsayin sabon shugaban NIPSS
A wani labarin, Majalisar Dattawar Najeriya ta tabbatar da Farfesa Ayo. O. Omotayo a matsayin Direkta Janar ta Cibiyar Koyar Ta Manyan Ma'aikata, NIPSS da ke Kuru, Jihar Plateau.
An samu wannan bayanin ne ta wata takarda wacce hadimin watsa labarai na musamman ga shugaban majalisar tarayya, Ezrel Tabiowo, a ranar Talata ya saki.
A cewar sanarwar, an tabbatar da Omotayo ne bayan an yi nazari kan rahoton kwamitocin Ayyukan Gwamnati da Daidaito wurin nadin mukami da ayyukan gwamnati.
Asali: Legit.ng