Da duminsa: Hukumar shige da fice ta Najeriya ta saki fasfotin Odili
- Hukumar shige ta fice ta Najeriya ta saki fasfotin tsohon gwamnan jihar Ribas, Peter Odili
- Lauyan hukumar shige da ficen ta Najeriya, Jimoh Adamu ya tabbatar da cewa diyar Odili Njideka Nwosu-Iheme ta karba fasfotin
- A cewar Adamu, takardar da ya bayyana wa alkali ta nuna cewa an karba fasfotin a hedkwatar NIS a ranar 20 ga watan Daisamban 2020
Abuja - Hukumar shige da fice ta Najeriya, NIS, ta saki fasfotin fitar kasar waje na tsohon gwamnan jihar Ribas, Peter Odili, wanda ta kwace kwanakin baya, The Nation ta ruwaito hakan.
Lauyan NIS, Jimoh Adamu, ya sanar da babbar kotun tarayyan da ke Abuja a ranar Litinin cewa, diyar Odili, Njideka Nwosu-Iheme, alkalin wata babbar kotu da ke Abuja ta karba fasfotin mahaifin ta a ranar 20 ga watan Daisamban 2020 a hedkwatar NIS da ke Abuja.

Kara karanta wannan
'Yancin mata ne: Gwamnatin Buhari ta magantu kan batun hana sanya Hijabi a makarantun Kwara

Source: UGC
Adamu, wanda ya shigar da bukatar a ranar Juma'a, ya bayyana takardar da Odili ya bayyana a matsayin shaidar cewa ya samu fasfotinsa, The Nation ta ruwaito hakan.
Mai shari'a Inyang Ekwo, wanda shari'ar ke hannunsa, a ranar Litinin ya ce sabuwar bukatar har yanzu ba a kawo ta a gaban kotun ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng