Baki yake yanka wuya: Minista ya kai ‘yan jarida kotu, ya ce a biya shi diyyar N100bn

Baki yake yanka wuya: Minista ya kai ‘yan jarida kotu, ya ce a biya shi diyyar N100bn

  • Ministan yada labarai da al’adu na kasa, Lai Mohammed ya kai karar wani gidan jarida a Abuja
  • Lai Mohammed ya maka mawallafi da editan Pointblank News zuwa babban kotu da ke garin Abuja
  • Lauyoyi su na tuhumar Johnson Ude da Uduma Mba da kokarin batawa Ministan tarayyar suna

Abuja - Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta samu ganin takardar karar da Alhaji Lai Mohammed ya shigar a kotu, ya na zargin an yi masa kage.

Ministan tarayyar ya na tuhumar gidan jaridar da kitsa karya domin su bata masa suna, don haka ya nemi su biya tarar Naira biliyan 50 saboda ya rage zafi.

Takardar kotun ta nuna Ministan ya nemi wasu Naira biliyan 50 daga hannun wadanda yake kara.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Miyagu sun sace $4bn daga arzikin Najeriya a 2021, su na sayen makamai

Premium Times ta ce Lai Mohammed yana tuhumar mai wannan gidan jarida na Pointblank News, Johnson Ude da kuma wani editanta, Mista Uduma Mba.

Rahotannin da aka fitar a 2021

A cewar Ministan labaran, wadannan mutanen sun fitar da wasu labarai da su ke yawo a kafafen zamani da su ke zarginsa da hannu a wata badakalar N10bn.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An yi wa labarin da aka fitar a ranar 3 ga watan Agustan shekarar 2021 take da: “‘Lai Mohammed in N10 billion Fraud Scandal as ICPC swoops on NBC”.

Ministan labarai
Alhaji Lai Mohammed Hoto: www.bbc.com
Source: UGC

A ranar 11 ga watan Agustan, sai ga wani rahoton ‘‘Lai Mohammed, NBC head for showdown over N10 billion Fraud, Minister in Hot Deal with Interpol Most Wanted’

Lai ya ce wadannan rahotanni da aka fitar a kansa ba gaskiya ba ne, kage da sharri ne marasa tushi.

A cewar Ministan kasar, da gan-gan aka rika kitsa wadannan labarai na bogi da nufin ci masa zarafi, a bata masa suna, ya ce ba a taba samun shi da yin laifi ba.

Kara karanta wannan

Barka: Ministan Najeriya da ya tafi karo ilmi ya kammala Digir-gir a Jami’ar Birtaniya

Sun ki cire labarin

Tun a lokacin da labarin ya fito, Ministan ya aikawa jaridar takarda su janye labarin ta bakin lauyansa, Kunle Jalejaye, SAN, amma su ka yi masa kunnen kashi.

Wadannan labarai sun jawo ana yi wa Lai kallon mutumin banza. Lauyoyin Lai sun bukaci a hana jaridar buga labari a kan sa. Ba a sa ranar da za a fara shari’a ba.

A ba matashi takara

Kwanakin baya kun ji labarin yada wata kungiya ta huro wuta, ta na so a ba matashi kujerar Mataimakin shugaban kasa da sauran mukamai masu tsoka a 2023.

Shugaban Youth Engagement and Inclusion Agenda, Idris Aregbe yace su na son mataimakin shugaban kasa ya fito daga bangaren matasa domin a rika yi da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng