Zulum: Boko Haram za ta zama tamkar wasan yara idan aka bari ISWAP ta girma
- Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya bukaci Rundunar Sojojin Najeriya ta sauya dabarun yakinta da kungiyar ta'addanci na ISWAP
- Gwamna Zulum ya ce idan har ba a dauki mataki kwakkwara a kai ba ISWAP din za ta haifar da matsalar da ta fi na Boko Haram
- Zulum ya yi gargadin cewa ISWAP ta fi Boko Haram samun kudade, ta fi ta waye wa sannan tana kara karfi a wasu yankunan Jihar ta Borno
Jihar Borno - Farfesa Babagana Zulum, Gwamnan Jihar Borno, ya nuna damuwa game da kara karfi da kungiyar Islamic State in West African Province (ISWAP) ke yi, rahoton The Cable.
Gwamnan, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi game da mayar da yan hijira zuwa gidajensu da hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jiharsa a Abuja.
Tun a watan Janairu, Zulum ya yi gargadi cewa idan ba a dauki mataki game da ISWAP ba a Borno, 'ba mutanen yankin arewa maso gabas kawai zai shafa ba, kasar baki daya abin zai shafa.'
Da ya ke magana a ranar Alhamis, ya ce ya zama dole sojoji su sake dabarun yakinsu kan yadda za su yi galaba a kan ISWAP, ya kara da cewa kungiyar za ta yi barna fiye da Boko Haram idan aka bari ta girma.
Zulum ya ce:
"Na fada a baya cewa ISWAP na karfafa a wasu sassan jihar nan kuma lamari ne da ya shafi kowa. Ina? Tafkin Chadi da Kudancin Borno. Amma, na ji an ce an tura sojoji Kudancin Borno a jiya domin yakarsu. Amma ina tunanin wannan gargadi ne.
"Bai kamata mu bari ISWAP ta girma ba. ISWAP ta fi samun kudi, ta fi wayewa da ilimi, amma za mu yi duk mai yiwuwa don cin galaba kan ISWAP, idan ba haka ba, abin da Boko Haram ta yi zai zama tamkar wasan yara ne.
"Ya kamata Rundunar Sojojin Najeriya ta sake dabarun cin galaba kan ISWAP. ISWAP zai iya zama barazana ga kasar baki daya saboda yanayin yankin kudancin Afirka."
Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023
A wani rahoton, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce baya sa ran neman wata mukamin siyasa a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.
Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.
Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.
Asali: Legit.ng