Yanzu-yanzu: Mun gano masu daukar nauyin yan ta'addan Boko Haram guda 96, Lai
- Gwamnatin Najeriya ta bayyana nasarorin da ta samu wajen yaki da cin hanci da rashawa a shekarar da ta gabata
- Ministan Labarai ya bayyana adadin masu baiwa yan bindiga da yan ta'adda kudi da masu musu canji
- Za'a gurfanar da wasu daga cikinsu cikin yan makonni masu zuwa, cewar Alhaji Lai Mohammed
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa hukumar leken asirin kudade a Najeriya NFIU ta gano mutum 96 masu baiwa yan ta'adda kudi, musamman yan Boko Haram da ISWAP.
Gwamnati ta kara da cewa NFIU ta bankado mutum 424 dake aiki tare da masu daukar nauyin, kamfanoni 123 da kuma yan kasuwan canji 33.
Ministan Labarai da Al'adu, Alh. Lai Mohammed, ya bayyana haka a hira da manema labarai ranar Alhamis, 2 ga Febrairu, 2022, rahoton TheNation.
A cewarsa, nan ba da dadewa ba za'a gurfanar da mutum 45 cikinsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Lai Mohammed yace:
"Binciken NFIU, a 2020-2021, ya fallasa masu daukar nauyin ta'addanci 96 a Najeriya, abokan huldan masu daukan nauyin guda 424, kamfanoni 123, da yan kasuwan canji 33."
"Bugu da kari, an gano masu garkuwa da mutane 26 da masu hannu cikin laifin guda bakwai."
"Binciken ya taimaka wajen damke mutum 45 wadanda za'a gurfanar ba da dadewa ba kuma a kwace dukiyoyinsu."
Sanatan APC ya koka kan yawaitar garkuwa da mutane a ƙasar
A bangare guda, Adamu Aliero, sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya ya kwatanta garkuwa da mutanen da ke ta karuwa a kasa a matsayin abin kunya ga Najeriya.
Aliero ya yi wannan maganar ne ranar Laraba yayin wani taron muhawara da Bello Mandiya, Sanata mai wakiltar Katsina ta Kudu ya shirya.
Mandiya ya janyo hakalin takwarorinsa a kan garkuwa da fiye da mutane 30 da ‘yan bindiga suka yi a karamar hukumar Faskari da ke Jihar Katsina.
Asali: Legit.ng