Ruɗani: 'Ya'yana suna amfani da suna na da sa hannu na wajen damfarar al'umma, Sarki a Arewa ya koka

Ruɗani: 'Ya'yana suna amfani da suna na da sa hannu na wajen damfarar al'umma, Sarki a Arewa ya koka

  • Basaraken Masarautar Bunu a jihar Kogi, Adebayo Joseph Ikusemoro, ya koka kan yadda 'ya'yansa ke zambatar mutane da sunansa
  • Sarkin ya yi kira ga al'umma su rinƙa bincikawa da zaran wata takarda da sa hannunsa ta isa gare su, su tuntubi mai martaba kai tsaye
  • Sarkin ya zargi wasu daga cikin 'ya'yansa da amfani da sunansa da kuma takardarsa wajen yaudarar mutane kuɗi

Kogi - Babban Basaraken Bunu, a jihar Kogi, Adebayo Joseph Ikusemoro, ya yi zargin cewa wasu daga cikin 'ya'yansa na amfani da sunansa da kuma takardar Letterhead wajen yaudarar mutane.

Jaridar Tribune Online ta rahoto cewa Basaraken, wanda shi ne shugaban majalisar sarakunan Bunu, ya faɗi haka ne a wata sanarwa da babban ɗansa, Yarima Josiah Ikusemoro, ya raba wa manema labarai a Lokoja.

Kara karanta wannan

Ohworode na masarautar Olomu: Muhimman abubuwa 5 game da basarake mai shekara 105

Sarkin Bunu
Ruɗani: 'Ya'yana suna amfani da suna na da sa hannu na wajen damfarar al'umma, Sarki a Arewa ya koka Hoto: tribuneonlineng.com
Source: UGC

Sarkin ya yi ikirarin cewa wasu daga cikin 'ya'yan da ya haifa na amfani da tsufansa wajen aikata wannan mummunan laifi.

Basaraken ya zargi cewa wasun su na amfani da takaradarsa ta Letterhead wajen neman taimakon kuɗi da kuma amincewa da naɗin Dagatai ba tare da saninsa ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babu wanda na amince ya wakilce ni - Sarki

A sanarwar da ya fitar, Sarkin yace bai amince kowa ya rubuta takarda a madadinsa ba ko a madadin majalisar masarautar Bunu.

Kazalika ya jaddada cewa bai umarci ko ɗaya daga cikin 'ya'yansa su wakilce shi ko su yi wani aiki a madadinsa ba.

Sanarwan tace:

"Muna kira ga mutane su yi watsi da duk wata takarda da aka kai musu da sa hannu a madadin mai martaba Sarki, waɗan nan wasiku ba gaskiya ba ne, ƙarya ce."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu

"Muna rokom al'umma baki ɗaya da su gudanar da bincike da zaran makamancin haka ya iso gare su, ta hanyar tuntubar Mai Martaba kai tsaye, ba ta hannun 'ya'aynsa ba."

A wani labarin na daban kuma Matasa sun bayyana sunan gwamnan da suke zargi da hannu a harin yan bindiga

Matasan yankin karamar hukumar Shiroro sun zargi gwamnatin jihar Neja da laifi kan harin da yan bindiga suka kai yankin su.

A martanin da kungiyar matasa ta yi wa gwamnan jihar, matasan sun ce gwamnati na zargin mutane ne saboda kokarin boye gazawarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262