Zamu cika alƙawuran da muka yi wa kungiyar ASUU, Buhari ya sha alwashi
- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sha alwashin cewa gwamnatinsa zata cika duk alƙawuran da ta ɗaukar wa ASUU
- Buhari yace gwamnatinsa ba zata sake kuskuren da zai kawo wani yajin aiki ba, wanda ke kawo wa bangaren ilimi cikas
- Shugabannin majalisar haɗin kan addinai NIREC sun roki shugaban ya yi duk me yuwuwa wajen cika wa ASUU yarjejeniyarta
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yace gwamnatinsa zata cika alƙawuran da ta ɗaukarwa kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) domin kare yajin aiki dake kawo cikas a harkar ilimi.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa Buhari ya sha alwashin cika alƙawuran ne ranar Talata yayin da ya karɓi baƙuncin majalisar haɗin kan addinai, (NIREC), a fadarsa dake Abuja.

Kara karanta wannan
2023: Ina da yakinin zan lallasa Atiku, Saraki, da sauransu a zaɓe, Ɗan takara ya bugi kirji
NIREC ta kaiwa shugaban ziyara ne bisa jagorancin shugabanninta, mai martaba sarkin Musulmi, Alhaji Saad Abubakar III, da shugaban ƙungiyar kiristoci, Samson Ayokunle.

Source: Facebook
A jawabinsa, shugaba Buhari, ya nuna jin daɗinsa bisa saka bakin da NIREC ta yi a yajin aiki da ASUU ta shiga kwanakin baya.
Buhari yace yayin da gwamnati ke kokarin cika bukatun ASUU, ya kamata ƙungiyar ta tausaya ta duba kalubalen da ƙasa take ciki wajen yanke hukunci.
The Nation ta rahoto cewa Buhari yace:
"Ya kamata kungiyar ta yi la'akari da ƙalubalen da muke fuskanta. Amma duk da haka zamu yi iyakar iyawa wajen cika aƙawuran da muka yi."
"A bangaren kungiyar, ina fatan su yi hakuri su cigaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnati wajen warware abubuwan da suke a gaban mu."
"Kofar gwamnati a buɗe take a zauna a tattauna har a samu maslaha, kuma ina rokon ASUU da su kasance a shirye wajen tattaunawar maslaha domin goben 'ya'ayan mu da ƙasa ya yi kyau."

Kara karanta wannan
Yanzu-Yanzu: Gwamnan PDP a Arewa ya bayyana shirin da yake na gaje kujerar Buhari a 2023
Wane mataki gwamnatin take ɗauka don cika aƙawuran?
Shugaban yace tuni ya umarci shugaban ma'aikata, ministan ilimi da ministan kwadugo su ɗauki lamarin da NIREC ta gabatar da muhimmanci domin kare aukuwar yajin aiki a gaba.
Kazalika, Buhari yace ya karɓi bayanai daga ministan kwadugo kan cigaban da aka samu game da bukatun da ASUU ke nema a cika mata.
"Domin tabbatar da maganar mu, mun sakar musu kuɗi a lokuta da dama cikin watanni 6 da suka gabata. Game da shawo kan matsalolin da kuka gabatar mana, ministan kwadugo zai baku cikakken bayani."
Meyasa majalisar NIREC ta kaiwa Buhari Ziyara?
A wurin taron, Ayokunle, wanda ya yi jawabi a madadin NIREC, yace sun garzayo wajen shugaban ƙasa ne domin kare yajin aikin ASUU da ka iya taso wa da kuma nemo hanyar warware kalubalen ASUU.
Shugabannin NIREC sun roki shugaba Buhari da ya kawo ƙarshen alƙawuran da gwamnati ta yi wa ASUU, wanda ya haɗa da na shekarar 2009.

Kara karanta wannan
Abin da gwamnatin mu take yi don tabbatar da zaman lafiya ya dawo Zamfara cikin ƙanƙanin lokaci, Buhari
A wani labarin kuma Majalisar Dattawan Najeriya ta ɗaga darajar kwalejin fasaha zuwa jami'a a Arewa
Majalisar dattawa ta amince da manyan muhimman kudirori da suka shafi makarantun gaba da sakandire a Najeriya.
A zamanta na yau Talata, Sanatocin sun amince da ɗaga darajar kwalejin fasaha zuwa jami'a a jihar Kwara.
Asali: Legit.ng