‘Yan bindiga sun aika mutane 1, 192 barzahu, sun dauke 3, 348 cikin shekara 1 a Kaduna
- Alkaluman da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar ya nuna ‘yan bindiga sun kashe mutane fiye da 1, 000
- Rahoton da aka fitar ya nuna an yi garkuwa da Bayin Allah fiye da 3, 000 a Kaduna a shekarar bara
- Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida ya bayyana wannan a wani rahoto da ya gabatar dazu
Kaduna - Akalla mutane 1, 192 suka mutu a hannun ‘yan bindiga, sannan kuma an yi garkuwa da wasu mutum 3, 348 a jihar Kaduna a shekarar da ta wuce.
Jaridar Daily Trust ta ce gwamnatin jihar Kaduna ta fitar da wadannan alkaluma a makon nan.
Wannan bayani yana cikin rahoton harkar tsaro da aka fitar daga watan Junairu zuwa Disamban 2021 wanda kwamishinan tsaron cikin gida ya gabatar dazu.
Mista Samuel Aruwan ya gabatar da wannan rahoto ne ga Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a ranar Talata, 1 ga watan Fubrairu 2022.
Samuel Aruwan ya ce an samu mutuwar mutane 720 a yankin tsakiyar Kaduna a sakamakon garkuwa da mutane, rikicin kabilanci, da sauran tashin-tashina.
Blueprint ta ce wadanda aka kashe sun hada da maza 1, 038, mata 104 da kananan yara 50. Alkaluman sun nuna an samu karuwar mace-mace da sata a bana.
Har ila yau an tabbatar da satar shanu 10, 261 a shekarar baran, adadin satar da aka yi ya nunku.
Kwamishinan yake cewa an samu mace-mace har 406 a sakamakon rikicin garuruwa da satar mutane a yankin kudancin jihar Kaduna a shekarar da ta wuce.
Kiran Mai girma Nasir El-Rufai
Gwamna Nasir El-Rufai ya ce alkaluman da aka fitar sun nuna cewa kusan a kullum sai ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane tara a jihar Kaduna a shekarar 2021.
El-Rufai ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da sansanin sojoji a Arewa maso yamma makamancin wanda aka kafa domin yakar ‘yan Boko Haram.
“Kirkirar irin wannan sansani zai bada dama a bullowa sha’anin yakar rashin tsaro gada-gadan a jihohi shida da abin ya shafa.”
“Wannan zai taimakawa sojoji, ‘yan sanda, dakarun SS, ‘yan banga da sauran ‘yan sa-kai wajen yakar masu tada kafar-baya.”
- Malam Nasir El-Rufai
Hari a Zangon Kataf
A ranar Litinin ne aka ji cewa miyagun ‘Yan bindiga sun kuma shiga yankin Kurmin Masara a karamar hukumar Zangon-Kataf, a jihar Kaduna sun yi ta'adi.
Wannan ne hari na biyu da ‘Yan bindiga suka kai a kauyen a cikin kwanaki biyu da suka wuce.
Asali: Legit.ng