Mutane sun mutu a wani sabon Hatsarin Jirgin ruwa da ya sake aukuwa a Kano
- Akalla mutum biyu aka tabbatar sun rasu a wani sabon hatsarin jirgin ruwa da ya sake faruwa a ƙaramar hukumar Rimin Gado, jihar Kano
- Rahoto ya bayyana cewa Kwalekwalen mai ɗauke da fasinjoji ya kife ne a hanyarsa daga ƙauyen Zangon Durgu zuwa Kanya
- Hukumar kwana-kwana ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar hatsarin, tace ta ceto rayuwar wasu mutum biyu
Kano - An tabbatar da mutuwar mutum biyu a wani sabon hatsarin kwalekwalen gargajiya da ya auku a ƙauyen Zangon Durgu, ƙaramar hukumar Rimin Gado, jihar Kano.
Kakakin hukumar kwana-kwana ta jihar, Saminu Yusif Abdullahi, shi ne ya tabbatar da haka ga manema labarai, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Yace Kwalekwalen, wanda ya ɗauko mutum huɗu kacal, ya kife ne yayin da yake kan hanyar zuwa ƙauyen Kanya daga Zangon Durgu.
Ya ƙara da cewa wani bawan Allah ɗan kamanin shekara 35, Sani Shitu, da kuma Jabir Sani sun tsira da rayuwarsu yayin da jami'an hukumar kwana-kwana suka kai ɗauki kuma suka ceto su.
Abdullahi yace Jami'an da suka kai ɗauki sun tabbatar da rasuwar Sha’aban Bala da kuma Rabi’u Bashari a hatsarin.
Kakakin hukumar ya ce:
"Mun miƙa gawar mutum biyun da suka rasa rayukan su ga shugaban ƙaramar hukumar Rimin Gado, Shafi’u Abdullahi Gulu."
Wannan ba shi ne na farko ba
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa a watan Disamba, 2021, wani kwalekwale da ya ɗakko fasinjoji da yawa mafi yawancin su ɗaliban Islamiyya ya yi hatsari a kan hanyarsa daga Badau zuwa Ɓagwai.
Lamarin wanda ya lakume rayukan mutum sama da 40, ya sa gwamnatin jihar Kano ta dakatar da zirga-zirgan jiragen ruwa a yankin baki ɗaya.
Kazalika makamancin wannan hatsarin ya taɓa faruwa shekaru 13 da suka shuɗe a Ɓagwai, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
A wani labarin na daban kuma Ɓarayi sun fasa Hostel ɗin mata a jami'ar BUK, sun aikata mummunar ta'asa
Wasu Barayi sun kutsa cikin dakin kwanan ɗalibai mata a jami'ar Bayero University Kano, sun sace manyan wayoyi.
Ɗaliban da lamarin ya shafa sun shiga matuƙar damuwa, domin har da sabbin wayoyin IPone daga cikin waɗan da aka sace.
Asali: Legit.ng