‘Yan bindiga sun sake dawowa Kaduna, sun yi ta’adi sa’a 24 bayan sun hallaka Bayin Allah
- Miyagun ‘Yan bindiga sun kuma shiga yankin Kurmin Masara a karamar hukumar Zangon-Kataf
- Wannan ne hari na biyu da ‘Yan bindiga suka kai a kauyen a cikin kwanaki biyu da suka wuce kenan
- Mazauna Atisa sun tabbatarwa manema labarai cewa an kai kusan sa’o’i biyu su na jin harbe-harbe
Kaduna - An tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kai hari a wani kauye da ake kira Atisa a garin Kurmin Masara da ke karamar hukumar Zangon-Kataf.
Rahotannin da mu ka samu daga jaridar Daily Trust dazu sun tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun aukawa wannan kauye ne cikin daren ranar Talatar nan.
Majiya daga karamar hukumar Zangon-Kataf a jihar Kaduna sun ce an ji harbe-harben bindiga a yankin Atisa a ranar Litinin, 31 ga watan Junairu, 2022.
Wani mazaunin wannan karkara ya shaidawa manema labarai cewa sun yi ta jin karar bindiga har karfe 11:45, kuma ana zargin miyagu ne suke ta’adi.
An shafe fiye da sa’a guda ana jin wannan harbe-harbe ba tare da an ji labarin kawo dauki ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“‘Yan bindigan sun zo ne da kusan karfe 9:50 na dare, su ka fara harbi a iska. Yanzu haka da nake yi maka magana, ina cigaba da jin karar tashin bindigogi.”
“Saboda mafi yawan mazauna sun bar gidajensu a Kurmin Masara a jiya (Lahadi), shiyasa maharan suka je Atisa, kauyen da ke kusa da Kurmin Masara.”
- Wani mazaunin yankin
"So ake a karar da mu"
Wani jagoran matasa na kasar Aytap, Gabriel Joseph ya tabbatar da cewa an kai masu hari, ya ce burin ‘yan bindigan shi ne su ga karshensu baki daya a yankin.
Harajin N24m da yan bindiga suka mana: Muna tsoron abin da zai biyo baya idan ba mu biya ba, Mutanen Zamfara
Punch ta rahoto Gabriel Joseph yana kira ga gwamnati ta dauki matakin da ya kamata domin ta kare rayukan al’ummarta da kuma dukiyoyinsu a jihar Kaduna.
Zuwa safiyar yau, Legit.ng Hausa ba ta samu labarin adadin mutanen da aka hallaka ko raunata a sakamakon wannan hari ba, ana sauraron jin ta bakin hukuma.
An kashe mutane a ranar Lahadi
Hakan ya na zuwa ne jim kadan bayan an samu labarin an kashe mutane 11 a garin na Kurmin Masara. A jiya ake makokin wadanda aka bi aka kashe su na barci.
A daren Lahadin da ta wuce, an samu wasu miyagun da suka shiga Zangon-Kataf, suka hallaka Bayin Allah, sannan su ka cinnawa gidajen mutane da-dama wuta.
Asali: Legit.ng