Da duminsa: Bayan Hanifa, an sake kashe wata yarinya a jihar Kano: Gwamna Ganduje
- Yayinda ake zaman shari'a kan makashin Hanifa, wani mutumi ya hallaka yar shekara 12 a jihar Kano
- Gwamnan jihar ya tabbatar da cewa shi ma an damkeshi kuma zai gurfana gaban kotu
- Hukumar kare hakkin bil adama a Najeriya ta yi Alla-wadai da wannan kashe-kashen kananan yara dake faruwa
Kano - Bayan labarin kisan Hanifa Abubakar a jihar Kano, Gwamna Abdullahi Ganduje, jiya, ya tabbatar da kisan wata yar budurwa kuma mai suna Zuwaira Gambo, a jihar.
Ganduje ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin Sakataren hukumar kare hakkin dan Adam, Mr Tony Ojukwu, wanda ya samu wakilcin Abubakar Muhammad, rahoton Vanguard.
Ya kai ziyarar jaje ne bisa kisan gillan da shugaban makaranta ya yiwa Hanifa Abubakar.
A jawabin da sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar, ya saki, Gwamnan yace jami'an tsaro tuni sun damke mutumin da ya kashe Zuwaira.
A cewarsa:
"Akwai wani sabon da ya faru inda wani mutumi ya kashe 'yar shekara 12, Zuwaira Gambo. Mun damkeshi sakamakon bibiyarsa da jami'an tsaro suka yi."
"Muna bibiyar lamarin tare da na Hanifa. Kuma mun sa ido sai an yi adalci.
Shugaban NHRC ya jinjinawa Gwamnan Kano bisa zaburarsa wajen ganin an tabbatar da adalci kan lamarin Hanifa.
Iyayen mutumin da ya kashe Hanifa sun gudu daga gidansu saboda tsoron hari
Wani rahoton Daily Trust ya nuna cewa iyayen mutumin da ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai shekaru 5, Abdulmalik Tanko, sun gudu sun bar gidansu kan tsoron kai masu farmaki.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a lokacin da ta ziyarci yankunan Tudunwada da Tudun Murtala inda daga nan ne Abdulmalik ya fito kuma a nan ne gidansu yake, makwabta sun gaza bayar da bayani kan inda iyayensa suka shiga.
Dan majalisa daga Gombe ya lissafo gwanayensa, ya ce daya daga cikinsu ne ya cancanci ya gaji Buhari
Majiyoyi na kusa da iyalan sun bayyana cewa an yi yunkurin kaiwa iyayen Abdulmalik hari sakamakon sacewa da kashe Hanifa da ya yi. Wannan lamari ya sa iyayensa suka gudu suka bar gidansu.
Asali: Legit.ng