Ke duniya: Yaro mai shekara 13 ya soka wa matashi mai shekara 19 wuka a Borno
- Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta damke wani yaro mai shekaru 13 da laifin soka wa wani matashi mai shekaru 19 wuka a ciki
- Abdullahi Sanusi ya na siyar da rake ne yayin da matashin a siya raken sa amma ya hana shi kudi, daga tambayarsa ya dinga jibgarsa
- Abdullahi bai yi wasa ba ya soka wa matashin wuka a ciki, lamarin da yasa ya fadi warwas aka mika shi asibitin Maiduguri inda yace ga garin ku
Borno - Rundunar 'yan sandan Jihar Borno ta cafke wani yaro mai shekaru 13 mai suna Abdullahi Sanusi bisa zargin sa da halaka wani matashi mai shekaru 19 a kan kin biyan sa kudin raken da yake sayarwa, TheCable ta ruwaito hakan.
Kamar yadda 'yan sandan suka bayyana, wanda lamarin ya auku a kansa, a ranar Laraba, "ya yi amfani da karfi" ta hanyar kwace rake daga hannun wanda ake zargi ba tare da ya biya ba, sai dai lokacin da ya nemi ya biya sa kudin sa, ya rufe sa da duka.
TheCable ta ruwaito cewa, 'yan sanda sun bada labarin yadda wanda ake zargin yayi amfani da wukar da yake datsa raken ya soki wuyan matashinn mai suna Muhammad Abdullahi.
Yayin jawabi ga manema labarai a ranar Juma'a, Abdul Umar, kwamishanan 'yan sandan jihar Borno, ya bayyana yadda wanda al'amarin ya auku a kan shi ya mutu a Asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri (UMTH).
"A rana mai kamar yau(19/01/2022) misalin karfe 5:00 na yamma, wani yaro dan shekaru 13 mai suna Abdullahi Sanusi ya yi amfani da wuka mai kaifi wadda ya ke amfani da ita domin datsa rake ya lumawa wani saurayi Muhammad Abdullahi mai shekaru 19 wuka a wuyan sa a wani guri da akewa lakabi da Gidan Dambe," a cewar kwamishinan.
"A sanadiyyar hakan, wanda lamarin ya auku da shi ya samu rauni. An yi kokarin ceto ran sa ta hanyar garzayawa da shi asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri (UMTH) dan samun taimakon gaggawa inda ya sheka lahira a ranar.
"Wanda ake zargin ya bayyana yadda mamacin ya kwace masa rake sannan yaki biyan sa kudi, sai dai yayin da ya bukaci ya biya sa hakkin sa ya hau jibgar sa a sanadin haka ne ya luma masa wuka," ya kara da cewa.
A wani lamari makamancin haka, kwamishinan ya tabbatar da hakfe Ahmad Umar Goni, wanda yake matakin kusa da karshe (SS2)a sakandaren Elkenemy College of Islamic Theology, bisa zargin sa da amfani da reza wurin yanka wuyan Jibril Sadi Mato, wanda yake matakin farko(JSS1) a makarantar.
An dakatar da dagaci kan yi wa budurwa auren dole, cin zarafin mahaifin ta da nada mata duka
A wani labari na daban, masarautar Minna ta dakatar da dagacin Allawa da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja, Mallam Bello Haruna, kan auren dole da kuma rashin biyayya ga masarautar.
A wasikar da masarautar ta aike ta hannun mataimakin sakataren ta, Usman Umaru Guni, kuma Daily Trust ta gani, ta ce basaraken ya yi wa wata yarinya auren dole, ya tozarta mahaifin ta kuma ya umarci 'yan sa kai da su lakada mata mugun duka.
Ana zargin dagacin da rashin biyayya ta yadda ya ki amsa kiran da aka yi masa zuwa fadar sarki domin yin bayani game da korafin sa da aka kai.
Asali: Legit.ng