Da Dumi-Dumi: Ba zan ɓata lokaci na wajen rattaba hannu kan hukunci kashe wanda ya halaka Hanifa, Ganduje
- Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, yace ba zai yi wata-wata ba wajen sanya hannun kan hukuncin kashe makashin Hanifa
- Ganduje wanda ya jagoranci tawagar gwamnatinsa zuwa gidan iyayen marigayya Hanifa, ya tabbatar da cewa kotu zata yi adalci
- Yace gwamnatinsa ta fara shirye-shirye, kuma suna da tabbacin shari'ar ba zata ɗauki lokaci ba
Kano - Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, yace ba zai bata lokaci ba wajen zartar da hukuncin kashe Abdulmalik Tanko, idan aka kawo shi kan teburinsa.
A ranar Litinin, Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya yi alƙawarin bin dokar da kwansutushin ya tanadar wajen zartar da hukuncin kisa kan Tanko, bayan kotu ta tabbatar.
Ganduje ya yi wannan furucin ne yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya tare da mataimakinsa, Nasuru Yusuf Gawuna, shugaban masu rinjayi na majalisa, Labaran Abdul da ƙusoshin gwamnati zuwa gidan iyayen Hanifa.
Vanguard ta rahoto Gwamna Ganduje yace:
"Mun samu kyakkyawan tabbaci daga kotun dake suararon ƙarar cewa za'a yi adalci kan lamarin. Babu ƙashin da ya fi karfin a taunasa."
"Duk wanda aka tabbatar ya aikata wannan ɗanyen aiki, to za'a kashe shi ba tare da ɓata lokaci ba. A bangaren mu, tuni muka fara shirye-shirye."
"Doka tace bayan kotu ta yanke hukuncin kisa, gwamna ke da ikon zartar da hukuncin kan wanda ya aikata laifin. Dan haka ina tabbatar muku ko daƙiƙa ɗaya ba zan ɓata ba."
Shin za'a dinga jan shari'ar a kotu?
Game da yanayin tafiyar shari'ar, gwamnan ya kara jaddada cewa ba za'a tsaya wani kace nace ba wajen yanke hukunci da yi wa Hanifa da iyalanta adalci.
Kazalika kan abin da ya faru da makarantar da Hanifa ke karatu, Ganduje ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta yi abin da ya dace.
Kano: Sheikh Pantami ya yi magana kan kisan Hanifa Abubakar, ya faɗi masifun da irin haka ke jefa al'umma
Uwar gidan shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta goyi bayan zartar da hukuncin kisa kan mutumin a bainar jama'a.
A wani labarin kuma Minista Sheikh Pantami ya yi magana kan kisan Hanifa, ya faɗi masifun da irin haka ke jefa al'umma
Malam Isa Pantami, ya bayyana cewa taɓa hakkin kananan yara babban laifi ne dake tsokano fushin Allah mai girma.
Ministan sadarwa yace ko a ranar Lahira, lallashin kananan yara ake su shiga Aljanna sabida darajarsu, amma suna cewa sai sun ga iyayen su.
Asali: Legit.ng