Kotu ta yankewa wasu masu walder 4 daurin shekaru 7 a kurkuku saboda satar N15m

Kotu ta yankewa wasu masu walder 4 daurin shekaru 7 a kurkuku saboda satar N15m

  • EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa ta gama shari’a da wasu ‘yan welder a Benin
  • Kotu ta kama wadanda ake kara da laifi, ta yanke masu hukuncin shekaru bakwai a gidan maza
  • Hukumar ta yi dace Alkali ya aika mutane hudun a gidan yari ne saboda sun sace kudin kungiya

Edo - Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon-kasa a Najeriya tayi nasarar aika wasu mutane hudu gidan yari saboda laifin sata.

Kamar yadda EFCC ta bada sanarwa a shafinta na yanar gizo, Alkali Ohimai Ovbiagele ya zartar da daurin shekaru 15 a gidan yari a kan wasu masu walda.

A ranar 21 ga watan Junairu 2020, Mai shari’a Ohimai Ovbiagele na babban kotun tarayya da ke garin Benin ya samu wadannan mutanen hudu da laifi.

Kara karanta wannan

Labari ne mai ban tsoro - Dattawan arewa sun yi Allah wadai da kisan Hanifa

Wadanda aka yankewa wannan hukunci sun hada da Isaac Ogundimu da John Odaro. Sai kuma wani Andrew Egharevba da kuma Mista Omorogbe Jacob.

Alkali ya samu wadannan mutane da shugabannin kungiyar masu walda na reshen jihar Edo ne, da laifin sace N15m daga cikin asusun kungiyar ESWA.

Masu walder
Shugabannin 'Yan kungiyar ESWA a Edo Hoto: officialefcc
Asali: Facebook

Gwamnatin jihar Edo ta ware miliyoyin kudi domin a karfafawa masu sana’ar walda. Amma wadannan mutane hudu suka hada-kai, suka yi gaba da kudin.

Alkali ya bukaci su je gidan yari na shekaru bakwai, ko kuma su dawo da N650, 000.

Tarihin wannan shari’ar

Tun a watan Oktoban 2017 ake shari’a tsakanin hukumar EFCC da shugabannin ‘yan waldan na Edo.

Lauyan da ya tsayawa EFCC a kotu ya fadawa Alkali cewa tsakanin Junairu zuwa Disamban 2016, wadannan mutane sun aikata laifuffuka 15 na sata da sauransu.

Kara karanta wannan

Takarar shugaban kasa a 2023: Babatu 3 da Tinubu ya yi da ka iya sa ya fadi a 2023

Wadannan laifuffuka da ake tuhumar masu waldan da aikatawa sun sabawa sashe na 383 (1)(a) da kuma sashe na 516 na final kwad na dokokin kasar Bendel.

A wancan lokaci, Ohimai Ovbiagele ya bada belin wadanda ake tuhuma da laifi a kan N500, 000. Dukkaninsu sun amsa cewa ba su aikata laifin da ake zargi ba.

Mashood Abiola bai ci guba ba

Bayan shekara da shekaru ana zargin guba aka ba Cif Mashood Abiola, Janar Abussalami Abubakar ya bada cikakken labarin mutuwar 'dan siyasar.

Abussalami Abubakar ya ce Abiola ya fara rashin lafiye ne yayin da yake ganawa da wasu Amurkawa, daga nan aka kai shi asibiti, inda ya rasu a nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng