Makircin 'yan siyasa: Bayan shekaru 3, an wanke Sanata daga zargin lalata da matar aure

Makircin 'yan siyasa: Bayan shekaru 3, an wanke Sanata daga zargin lalata da matar aure

  • Zargin da ake yi wa Godiya Akwashiki na neman matar Danladi Envulanza sam ba gaskiya ba ne
  • ‘Yan sanda sun ce Amina Danladi Halilu ba ta iya tabbatar da cewa Sanata Akwashiki ya nema ta ba
  • A karshe ma sai dai aka gano mai gidanta, Danladi Envulanza da wasu ne suka shirya tuggu

Abuja - An gano cewa Sanatan da ake zargi da laifin lalata da matar aure, bai aikata laifin da ake tuhumarsa da aikatawa ba, sharrin ‘yan siyasa ne kurum.

Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto a ranar 20 ga watan Junairu 2022 da ya bayyana cewa an gano gaskiyar abin da ya faru da Sanata Godiya Akwashiki.

Jami’an ‘yan sanda suka bayyana wannan bayan jaridar sun bukaci sakamakon binciken da suka yi.Akwashiki ya tabbatar da hakan da aka nemi jin ta bakinsa.

Kara karanta wannan

An dakatar da dagaci kan yi wa budurwa auren dole, cin zarafin mahaifin ta da nada mata duka

A lokacin da abin ya faru Godiya Akwashiki ya na kan kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawan jihar Nasarawa, kuma ya lashe zaben Sanata kenan.

Zargin da aka jefi Akwashiki da aikatawa

An zargi Sanata Akwashiki da laifin neman matar wani ‘dan siyasa daga jiharsa ta Nasarawa, Danladi Envulanza, wanda hakan ya sa aka ci masa mutunci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da bidiyo ya bayyana aka ga ‘dan majalisar na Nasarawa ta Arewa yana neman Amina Danladi Halilu a gidan mijinta, sai ‘yan iskan gari suka yi masa la-las.

Godiya Akwashiki
Sanatan APC, Godiya Akwashiki Hoto: www.pulse.ng
Asali: UGC

A farkon watan Maris a 2019, Amina Halilu ta shigar da karar Akwashiki wajen rundunar ‘yan sanda da ke Maitama a Abuja, ta ce ya nemi ya yi lalata da ita.

Ya aka ji shiru?

Ganin an dauki lokaci ba a sake jin labarin inda aka kwana a wannan kara ba, sai 'yan jaridar suka tuntubi rundunar ‘yan sanda domin jin inda aka kwana.

Kara karanta wannan

Hotunan makusancin ɗan ta'adda Turji, tare da wasu gwamnonin arewa ya tayar da ƙura

Wani jami’in ‘yan sanda a garin Abuja, Fom Pam Joseph a madadin kwamishinan da ke binciken masu manyan laifuffuka ya fadawa jaridar sakamakon bincikensu.

Sanata bai da laifi

A cewar Fom Pam Joseph, Misis Envulanza ba ta iya tabbatar da ikirarin da ta ke yi ba, sai dai ma aka samu mai gidanta da bata suna da aikata wasu laifuffukan.

‘Yan sanda sun samu Danladi Halilu Envulanza “m”, Jamilu Halilu “m” Abdullahi Aliyu Ogah “m”.” da aikat laiffukan da suka sabawa wasu sassa na dokar final kwad.

A cewar jami’an tsaro, ‘yan siyasan biyu sun jaye karar da aka kai a kotu, sun sasanta tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng