An tono badakalar Naira Biliyan 370 da aka tafka a kasafin kudin 2022 da Buhari ya sa hannu
- BudgIT ya yi ikirarin ya bankado badakalar da suke cikin kasafin kudin wannan shekarar ta 2022
- An yi mai-men kwangiloli kusan 500 a kasafin bana, hakan za su jawo ayi awon gaba da N370bn
- Binciken da aka yi ya nuna cewa ma’aikatun tarayya su na kakaba ayyukan bogi a kasafin kudinsu
Abuja - A ranar Litinin, 17 ga watan Junairu, 2022, BudgIT ta bayyana cewa ta gano an yi mai-men wasu ayyuka har 460 a kasafin kudin shekarar 2022.
BudgIT ta ce wadannan kwangiloli da aka maimaita a kundin kasafin kudin za su ci N378bn. Iyanu Fatoba ya bayyana wannan a wata sanarwa dazu.
Kamar yadda suka bayyana a shafinsu na Facebook, BudgIT sun ce akwai wasu kofofin satar dukiyar al’umma da aka bude a kundin kasafin kudin bana.
Daga ciki an ankarar da mutane cewa ma’aikatar muhalli ta ware N67.8m da sunan gina wuraren ajiye bindigogi a jihohi hudu, wanda wannan ba aikinta ba ne.
Kwangilolin bogi a Aso Rock?
Binciken da BudgIT ta yi, ya nuna cewa an kara kudin wasu kwangiloli na biliyoyi da za a yi a fadar shugaban kasa, daga ciki har da gini a asibitin Aso Villa.
N20.7m aka ware da nufin gina sashen shugaban kasa a asibitin da ke cikin fadar Aso Villa, sai dai kuma a halin yanzu akwai wannan sashe a asibitin a gine.
Akwai N28.72m da aka sa a kundin kasafin kudin shekarar 2022 na sayen na’urorin sukola biyu da kuma talabijin na kirar LG a gidan gwamnati da ke Legas.
Babura za su ci N1.3bn a 2022
Dubu ta cika: Wani mutum ya shiga hannu yayin da ya kashe yaransa uku ya adana gawarwakinsu a cikin firinji
National Agency for Great Green Wall da aka kafa domin magance matsalar cin kasa da samar da isasshen abinci za ta kashe N1.3bn a 2022 wajen sayen babura.
Shi ma wannan aiki na sayen babura da kafa fitulu a kan hanya da hukumar ta dauko ba ya cikin hurumin da aka ba ta a jihohi Arewacin Najeriya 11 da ta ke aiki.
A karshe BudgIT tayi kira ga gwamatin shugaba Muhammadu Buhari ta maida hankali wajen yin ayyukan da al’ummar kasar suke bukata a shekarar nan ta 2022.
Dokar zabe
A ranar Lahadin da ta wuce ne tsohon shugaban hukumar INEC, Farfesa Attahiru Jega ya bada shawarar a gyara dokar zabe na kasa kafin a shirya zaben 2023.
Farfesa Jega ya na ganin akwai wasu abubuwan alheri a kudirin zaben da shugaban kasa yi watsi da shi saboda wasu kura-kurai da aka samu tattare da shi.
Asali: Legit.ng