'Yar Shugaban kasa, Zahra Buhari, ta yi magana kan meyasa ba'a son Maza na kuka
2 - tsawon mintuna
- Diyar Shugaban kasa ta yi bayani yadda take mamakin dalilin da yasa ba'a son ganin maza na kuka
- A cewarta, zuciyar mace daya ne da namiji saboda haka ya kamata maza su rika kuka
- Yan Najeriya a kafafen ra'ayi da sada zumunta sun yi martani kan wannan maganar da tayi
Zahra Buhari-Indimi, 'diyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa tana mamakin dalilin da yasa ba a son ganin maza suna kuka duk da su ma yan Adam ne kaman matan.
A tsokacin da tayi a shafinta na Instagram, Zahra ta yi addu'an Idan Allah ya yarda a AlJannah ba za muyi kuka ba.
A hoton da ta daura dauke da rubutun larabci da turanci mai cewa 'A Aljannah, ba zamu taba kuka ba'.
A kasa sai ta kara da jawabin cewa:
"Wani lokaci sai kayi mamakin me yasa ba'a son ganin maza na kuka?....Idan mace na jin shauki, shi ma namiji yana ji."
Martanin yan Najeriya
Nura C Ibrahim:
Allah sarki saboda idan maza sukayi kuka lamari ya baci sune suke rarrashin mata kuma sannan aga suna kuka
Aliyu Santuraki Yunusa:
Kitambayi babanki lokutan dasha Kaye azabe miyasashi kuka
Mohammed Husaini JB:
In namiji daya yayi kuka sai mata goma sunyi
Sheikh Ahmad Sadees:
Ki tambayi lusarin babanki Danliti mugu
Idris Musa Nyabo:
Shiyasa mai dattin hula ya yaudaremu da kuka kenan?
Sulaiman Azare:
A madadin Baba manjo daya Jagoranci tawagar ƙare kukan maza a 2015 ke kuma kikeson sai an cigaba muna Allah wadai da wannan yunƙuri naki.
Yakub Chamba Sani:
2011 da ubanki yaji kayi baiyi ba saboda kunshiga daula kun manta ko,
Asali: Legit.ng