Ma’aikata sun fara salati, Gwamnatin Buhari za ta karbi aron N620bn daga asusun fansho
- Gwamnatin Tarayya ta na shirin ta karbi bashin Naira Biliyan 620 daga asusun fanshon ma’aikata
- Ana bukatar a kashe Naira tiriliyan 7.7 wajen gina abubuwan more rayuwa tsakanin 2021 da 2025
- Idan gwamnati ta samu dama daga masu kula da kudin, za a ci bashin domin a samar da tituna da dogo
Abuja - Wani rahoto daga Punch ya ce Gwamnatin tarayya ta na shirin cin bashin fam $1.5bn (N620bn) daga asusun fansho domin samar da hanyoyi.
Gwamnatin Muhammadu Buhari ta na neman hanyar da za ta hada Naira tiriliyan 7.73 da za a kashe wajen bunkasa harkar sufuri nan da shekaru biyar.
Gwamnati ta na so ta karbi aron abin da ke cikin asusun fanshon ma’aikata da nufin biyan kudin aiwatar da wadannan ayyuka daga shekarar 2021 zuwa 2025.
Ana sa ran abin da ke asusun fanshon zai karu da kimanin kashi 15% a cikin shekaru biyar.
Jaridar tace wannan shiri da gwamnati ta ke yi yana cikin kundi na farko na takardar tsarin tattalin arzikin kasa na ‘National Development Plan 2021-2025.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga ina za a samu N7.7tr?
Wadannan kudi har Naira tiriliyan 7.73 da gwamnati ta ke nema za su fito ne daga asusun Presidential Infrastructure Development da kudin fanshon.
Sai dai gwamnati ba za ta dauki kudin haka ba sai idan ma’aikatan da suke da hakki sun yarda su yi amfani da kudin na su wajen bunkasa harkar sufuri a kasar.
Akwai adadin abin da za a iya dauka daga cikin kudin da aka yi wa ma’aikata tanadi idan sun yi ritaya. Daga wannan kaso ne gwamnatin tarayya za ta karbi aro.
TV360 ta ce Gwamnatin Muhammadu Buhari tayi amfani da kudin satar Abacha da suka dawo, $321m wajen aikin titin Abuja-Kano, Legas-Ibadan da gadar Neja.
Ka'idar neman aron da aka sa
“Za a samu karin $1.5bn (N620bn) daga asusun fansho, idan aka kaddara darajar abin da ke asusun na fiye da $31.3bn a 2019 zai rika karuwa da 15% a shekara.”
“Sai masu kula da fanshon sun amince da dukiyar a cikin ginin abubuwan more rayuwa."
An yi nadin mukamai
A makon nan ne aka ji cewa Gwamnatin tarayya ta amince da nadin Mathew Lawrence Pwajok a matsayin sabon darektan rikon-kwarya a hukumar nan ta NAMA.
Nadin na Mathew Lawrence Pwajok yana zuwa ne yayin da wa’adin shugaba mai-ci, Kyatfin Fola Akinkuotu ya zo karshe a watan Junairun nan na 2022 da ake ciki.
Asali: Legit.ng