Miyagun ‘Yan bindiga sun sace Mai jego da ‘Diyarta kafin tayi 40 a garin shugaban kasa
- Miyagun ‘Yan bindiga sun sace wata mai jego a wata unguwa da ke garin Danmusa a jihar Katsina
- Rahotanni sun ce an yi awon-gaba da wannan mai jego da ‘diyar da take shayarwa mai suna Farha
- Wata Baiwar Allah mai suna Khadijah wanda kanwar mai jegon ce, tana cikin wadanda aka dauke
Katsina - Wani mummunan lamari ya faru a wani kauye da ke cikin jihar Katsina – inda nan ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fito.
Rahoton da jaridar Katsina Post ta fitar a ranar Talata, 11 ga watan Junairu, 2022, ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun dauke wata mata mai shayarwa.
Miyagun ‘yan bindigan sun yi awon-gaba da wannan mai jego mai suna Malama Saratu da kuma ‘diyar da take shayarwa a ranar Litinin cikin dare.
An bada sunan jaririyar ‘yar wata daya a Duniya da wadannan ‘yan bindigan suka dauke a wata unguwa da ke garin Danmusa, jihar Katsina da Farha.
Haka zalika wadannan miyagu sun hada da ‘yaruwar mai jegon mai suna Khadijah (wanda aka fi sani da Mama), sun tafi da su, har yau babu labarinsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga zuwa ziyara
Blueink News Hausa tace an sace wadannan mutane ne yayin da suke dawowa daga unguwar Sabuwar Abuja zuwa gidansu a unguwar Sabon Layi.
Majiyoyi da-dama sun tabbatar da an dauke wadannan mutanen ne a yankin Sabuwar Abuja da ke karamar hukumar Danmusa wajen karfe 7:00 na dare.
Jama'a sun yi tir
A halin yanzu mutane su na ta Allah-wadai da wadannan danyen aikin, tare da addu’ar kubutar da wadannan mata uku da ake zargin an yi garkuwa da su.
“Ya salaam. Allah Ya Bayyanasu, Ya kubutar da su..Aamin”
- Muhammad Nura Rafindadi
“Allah ya kubutar da su.”
- Auwal Tasiu
“A Danmusa LG akayi unguwarmu watau Sabuwar Abuja.”
- Sadiq Danmusa
Shi kuma wani Bawan Allah ya ce:
“Innalillahi wa'innah ilahirraji un kai wai nikan a INA zamusa kammune ???
An caccaki Bashir Ahmaad
A jiya aka ji yadda mutane suka yi wa Hadimin Shugaban Najeriya, Bashir Ahmaad rubdugu saboda yace sai nan gaba za a ga amfanin Muhammadu Buhari.
Bashir Ahmaad, ya ce ’yan Najeriya ba za su ga amfanin mulkin Buhari a yanzu ba, sai nan gaba domin ya aza gwamnatin tarayya a kan turbar da za a ci moriya.
Asali: Legit.ng