Muazu Babangida Makaryaci ne, bamu yiwa Arewa alkawarin tikitin kujeran Shugaban kasa ba, PDP

Muazu Babangida Makaryaci ne, bamu yiwa Arewa alkawarin tikitin kujeran Shugaban kasa ba, PDP

  • Uwar Jam'iyyar adawa ta PDP ta yi watsi da jawabin wani tsohon gwamna da yayi kan tikitin shugaban kasa a 2023
  • Muazu Babangida ya bayyana a wani jawabi cewa PDP ta yi alkawarin baiwa Arewa kujerar Shugaban kasa
  • PDP tace har yanzu bata lamuncewa ko wani yanki tikitin zaben ba

Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta yi martani kan jawabin tsohon Gwamnan jihar Neja, Muazu Aliyu Babangida cewa an baiwa Arewa tikitin kujerar shugaban kasa a 2023.

Kakakin jam'iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya yi watsi da wannan magana inda yace wannan karya ne kuma jam'iyyar bata yi hakan da kowa ba.

Jam'iyyar PDP
Muazu Babangida Makaryaci ne, bamu yiwa Arewa alkawarin tikitin kujeran Shugaban kasa ba, PDP
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabin da ya saki ranar Asabar a shafin PDP na Facebook, yace jam'iyyar bata baiwa ko wani yanki tikici ba.

Kara karanta wannan

Halifan Tijjaniya na Duniya, Sheikh Tahir Bauchi, da manyan Maluma sun taru a Kano don addu'a

Yace:

"Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta samu labarin cewa wasu daidaikun mutane na ikirarin jam'iyyarmu ta baiwa wani yanki tikitin takarar kujerar Shugaban kasa."
"Wannan ba gaskiya bane kuma wannan ba matsayar jam'iyyar bace."
"Maganar gaskiya itace PDP bata baiwa kowani yanki tikici kujerar shugaban kasa ba."

Tsohon gwamnan jihar Neja, ya ce PDP za ta mika tikitin takarar shugaban kasarta a zaben 2023

Mun kawo muku cewa Tsohon gwamnan jihar Neja, Dr Babangida Aliyu, ya bayyana cewa jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta yanke shawarar sake mika tikitin shugaban kasa ga yankin arewa.

Hakan na zuwa ne duk da yarjejeniyar jam'iyyar adawar na cewa kowani dan takara zai iya tseren kujerar a zaben.

Aliyu ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a, 7 ga watan Janairu, lokacin da kungiyar goyon bayan Atiku suka ziyarce shi a garin Minna, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jigon PDP na zawarcin Yahaya Bello, ya ce jam’iyyar za ta nada shi shugaban kasa

Hakazalika tsohon gwamnan na Neja ya ce yana da yakinin nasarar kungiyar. Ya kuma basu tabbacin samun goyon bayansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng