Ba zaku tilasta wa yan Najeriya ba, Shugaba Buhari ya caccaki yan majalisu kan kundin zabe
- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya sake yin martani ga majalisar tarayya kan sabon kundin gyaran zabe 2021 da yaki sa wa hannu
- Shugaban yace ba zai yuwu a tilasta wa yan Najeeiya wata doka ba wajen fitar da gwani kuma ace ana mulkin demokaradiyya
- Buhari yace a shirye yake ya rattaba wa kudirin hannu da zaran yan majalisu sun sake aiki a kansa kuma sun aiko masa
Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yace shi a karan kansa bai amince da zaben yan tinke ba wajen fitar da ɗan takarar jam'iyyun siyasa.
Daily Trust tace ƙin amincewar da shugaba Buhari ya yi wa sabon kundin zabe da akai wa garambawul 2021 ya jawo cece kuce a faɗin ƙasar nan.
Majalisar dattawan tarayyan Najeriya ta yi yunkurin tsallake matakin Buhari na kin rattaba wa kudirin hannu kafin a ci ƙarfinta.
Da yake jawabi kan matakin da ya ɗauka a zantawarsa da kafar Channels TV kai tsaye, shugaba Buhari, yace ya kamata a samu zaɓi wajen fitar da ɗan takara a zabe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan ba demokaradiyya bane - Shugaba Buhari
Shugaban yace tilasta yin zaben kai tsaye kadai ya saba wa mulkin demokaraɗiyya.
Buhari yace:
"Ba zai yuwu ka tilasta wa mutane doka ba kuma kace kana mulkin demokaraɗiyya. Ya kamata ace akwai zabi, bai kamata mu tilasta dole sai an bi hanyar kai tsaye ba."
Shugaban ƙasan ya yi alkawarin cewa zai rattaba hannu a kan kudirin matukar yan majalsun tarayya suka sake aiki a kansa sannan kuma suka tura masa.
Kada ku dogara da gwamnati - Buhari ga matasa
Kazalika shugaba Buhari ya bukaci matasa kada su zauna suna tunanin gwamnati zata ba su aiki bayan kammala makaranta.
Buhari ya sha suka daga yan Najeriya ta kowane bangare lokacin da ya bayyana matasan Najeriya a matsayin sangartattu da ba su son moriya.
Da aka tambaye shi game da matasa a tattaunawa da Channels TV, Buhari yace:
"Ina fatan idan suka je makaranta, suka yi karatu sosai har suka samu shaidar kammala digiri, ba za su zauna tunanin gwamnati za ta samar musu aiki ba."
A wani labarin na daban kuma Khadijat yar kimanin shekara 38 ta bayyana shirinta na maye gurbin shugaba Buhari a zaɓen 2023
A tarihin Najeriya ba'a taba samun mace da ta zama shugaban ƙasa ba tun bayan samun yancin kai daga turawan mulkin mallaka a shekarar 1960.
Wata matashiya yar shekara 38, Khadijah Okunnu-Lamidi, ta bayyana sha'awarta na maye gurbin shugaba Buhari a babban zaben 2023 dake tafe.
Asali: Legit.ng