Bashir Tofa: Bayani a kan rayuwar Marigayin da hirar karshe da ya yi a kan mulkin Buhari
- A ranar 3 ga watan Junairu, 2022, aka samu labarin rasuwar dattijon Arewa, Alhaji Bashir Othman Tofa
- Legit.ng Hausa ta tattaro wasu daga cikin abubuwan da ya kamata a sani game da rayuwar Marigayin.
- An haifi Marigayin a birnin Kano a shekarar 1947 kuma ya yi karatunsa ne a gida Najeriya da Birtaniya
1. Haihuwa
An haifi Bashir Othman Tofa a ranar 20 ga watan Yuni,1947 a birnin Kano. Iyayensa bare-bari ne da suka zo Kano.
2. Karatu
Marigayi Bashir Othman Tofa ya fara karatun firamare a makarantar Shahuci Junior Primary da ke Kano.
Daga nan ya karasa karatun firamaren na sa a makarantar City Senior Primary School duk a cikin birni.
A 1962 Tofa ya tafi makarantar Provincial College, Kano, ya kuma yi nasarar kammalawa a shekarar 1966.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
3. Fita kasar waje
Tsakanin 1970 zuwa 1973, Tofa ya na Birtaniya, inda ya yi karatu a City of London College da ke Landan.
4. Aiki
A shekarar 1967 Marigayin ya samu aiki da kamfanin inshora na Royal Exchange Insurance company.
5. Siyasa
Tofa bai dade ya na aiki a kasar waje ba, bayan dawowarsa gida sai ya tsunduma cikin harkar siyasa.
A shekarar 1977 Bashir Tofa ya zama Kansila a Dawakin Tofa bayan an kirkiro kananan hukumomi.
Marigayi Tofa ya na cikin ‘yan majalisar da suka tsara kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1979.
Bayan aikin da suka yi a 1977, Tofa ya shiga jam’iyyar NPN da sojoji suka bada dama a dawo siyasa.
Tsakanin 1979 da 1983, Marigayin ya rike mukamai dabam-dabam a jam’iyyar NPN a reshen Kano da kasa.
Tofa ya taba zama Sakataren jam'iyyar NPN a reshen jihar Kano da sakataren kudin jam’iyyar na kasa.
6. Takarar shugaban kasa
Shekaru kusa ngoma bayan an yi juyin-mulki, Tofa ya shiga daya daga cikin jam’iyyun da sojoji suka kafa
Alhaji Tofa ya nemi takarar shugaban kasa a jam’iyyar NRC bayan an hana wasu shiga takara a 1992
Jam’iyyar NRC ba tayi nasara ba, alkaluma sun nuna MKO Abiola na jam’iyyar SDP ya doke ta har a Kano.
7. Dattijon Arewa
Daga baya Attajirin ya ajiye harkar siyasa, ya cigaba da kasuwancisa da kuma kare Arewacin Najeriya.
Hirar karshe da Bashir Tofa
A wata hira da ya yi da BBC, Tofa ya koka cewa gwamnatin Buhari ba ta daukar shawara kan batun tsaro.
Wannan hira a 2020 na cikin maganar da aka yi da shi na karshe inda yace kokarin gwamnati mai-ci, bai isa ba.
Marigayin ya tabo zancen zanga-zanga da wasu matasa ke yi domin ankarar da shugaba Muhammadu Buhari.
Asali: Legit.ng