Duk kashe-kashen da ake yi na matukar damuna, Buhari ya aike sakon jaje ga yan Najeriya

Duk kashe-kashen da ake yi na matukar damuna, Buhari ya aike sakon jaje ga yan Najeriya

  • Shugaba Buhari ya jajantawa yan Najeriya bisa kashe-kashen da ke faruwa a sakon sabuwar shekararsa
  • Shugaban kasan ya ce gwamnatinsa ta zuba makudan kudi wajen sayen makamai don kawar da yan bindiga
  • A cewarsa, matsalar tsaro na hana mutane ganin irin ayyuka da nasarorin da gwamnatinsa ke samu

FCT Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Gwamnatinsa ba zata gushe tana iyakan kokarinta wajen magance matsalar tsaron Najeriya ba.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne a jawabin murnar sabuwar shekarar da ya saki da yammacin Juma'a.

Ya ce yan Najeriya su yi hakuri, gwamnatinsa na hada kai da kasashen dake makwabta wajen samar da mafita daga cikin lamarin rashin tsaro.

Buhari ya aike sakon jaje ga yan Najeriya
Duk kashe-kashen da ake yi na matukar damuna, Buhari ya aike sakon jaje ga yan Najeriya Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

A sakon sabuwar shekara, Ganduje ya yi magana kan sasanci da Kwankwaso da tsagin Shekarau

Buhari ya aika sakon taz'iyyarsa ga iyalan jami'an tsaro da jama'an da suka rasa 'yan uwansu sakamakon matsalar tsaro.

A cewarsa:

"Ina son amfani da wannan dama wajen tunawa da karrama Sojoji, yan sanda, da sauran jami'an tsaron da suka rasa rayukansu wajen kare mutuncin kasar nan daga wajen yan ta'adda na gida da na waje, ina tabbatarwa iyalansu cewa sadaukarwan da sukayi ba zai tafi a banza ba."
"Hakazalika mun jajantawa yan Najeriya da suka rasa yan uwansu sakamakon rikicin tsaro a sassan Najeriya. Duk rayuwar da aka rasa sakamakon rashin tsaro na damuna a matsayin dan kasa kuma matsayin shugaban kasa."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng