Allah ya yiwa tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a, Dr Datti Ahmad, rasuwa
- Shahrarren Likita kuma dan gwagwarmaya, Dakta Datti Ahmad ya rigamu gidan gaskiya
- Manyan Maluma a jihar Kano da Najeriya sun yi alhinin mutuwarsa
- Da dama sun siffantashi mastayin wanda ba za'a taba mantawa da irin gudunmuwar da ya baiwa addinin Musulunci ba
Allah ya yiwa tsohon Shugaban Majalisar koli ta Shari'a a Najeriya (SCSN), Dr Datti Ahmad, rasuwa ranar Alhamis a jihar Kano.
Legit ta tattaro cewa Dr Datti ya rasu ne bayan rashin lafiya da yayi fama.
Diraktan tashar Sunna TV, Dr Abu Aisha Ibrahim Disina a jawabin ta'aziyyarsa ya bayyana cewa za'a yi Sallar jana'iza a Masallacin Al-Furqan dake Kano misalin karfe 10 na safe.
Ya siffanta marigayin a matsayin dan gwagwarmayan kare Musulmai a Najeriya.

Kara karanta wannan
Hotunan mai jinyan da ya sace motar Asibiti a jihar Kano bayan Yan sanda sun damkeshi
A cewarsa:
"Gwagwarmayar kare muradun Musulmai ba za ta manta da kai ba a Nigeria!! Janaza: 10:00am a Masallacin Alfurqan Kano.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Allah ya karbi aiyukanka, Ya kai haske kabarinka, Ya sanya Aljannah ce Makomarka.
Allah ka kiyayemu, mu 'yan baya, Ya sa mu cika da Imani."

Asali: Facebook
Ya taba takarar kujerar shugaban kasa
Marigayin, wanda Likita ne gabanin rasuwarsa ya taba takarar neman kujeran shugabancin kasa.
A 2013, Gwamnatin Jonathan ta nada shi cikin kwamitin da za tayi sulhu da yan Boko Haram amma yace ba zai yi ba saboda gwamnatin ba gaske take ba, a cewarsa.
Asali: Legit.ng