Matan Zamfara sun bada labarin yadda ‘Yan bindiga su ke kwanciya da su da karfi-da yaji

Matan Zamfara sun bada labarin yadda ‘Yan bindiga su ke kwanciya da su da karfi-da yaji

  • ‘Yan bindiga su na yin taron-dangi su yi lalata da mata da karfin tsiya a wasu kauyukan Zamfara
  • Miyagun ‘yan bindigan sun fitini yankin Tsafe, su na kwanciya da matan mutane da karfi-da yaji
  • Duk mata ko yarinyar da ta ce sam ba ta yarda ba, wadannan ‘yan bindiga za su aika ta barzahu

Zamfara - Matan da suka bar gidajensu saboda matsalar rashin tsaro a yankin Tsafe, jihar Zamfara, sun bayyana irin yadda ‘yan bindiga suke lalata da su.

A ‘yan kwanakin bayan nan, mata da yara da dama sun tsere daga gidajensu saboda hare-haren da ‘yan bindiga suke kai wa a kauyukan yankin Tsafe.

Matan da ke wadannan kauyuka sun bayyana cewa ‘yan bindiga na tilasta masu kwanciya da su. Jaridar Daily Trust ta fitar da wannan rahoto a ranar Larabar nan.

Kara karanta wannan

Zamfara: Mutane sun tsere daga gidajensu bayan 'yan bindiga sun kashe mutum 10 sun sace mata 33

Don dole mutane suke barin garuruwansu kamar yadda mazauna yankunan suka bayyana. Ana zargin wani Adamu Aleiro da yaransa ne ke yin wannan ta’adi.

Wannan gawurtaccen ‘dan bindiga, Aleiro, ya fitini kauyukan Tsafe da garuruwan Katsina. A 2018 aka kama wasu shanu fiye da 500 da ya sato a Neja da Kaduna.

Zamfara
Wasu 'Yan bindiga Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Abin da matan suke fada

“Su na taruwa su yi mana lalata, kuma idan wata mace ko yarinya ta ce masu a’a, nan take za su harbe ta.”
“An harbe mata da yawa saboda sun ki yarda ayi amfani da su.”

- Wata mata

“’Yan bindigan sun fito da wata mata daga gidan aurenta. Suka nemi keta mata mutunci, da ta ki yarda, sai suka harbe ta a kai, duk da mijinta ya lallabe su.”

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi kuskure, sun yi awon gaba da Jami’in tsaro, sun dauka Attajiri su ka sace

- Hajara ta shaidawa Daily Trust

“Bayan sun kashe ta, sai suka sake kawo hari a kauyen, za su kashe wadanda suka kai ta makabarta domin rufe ta, sai da aka birne ta a garin Tsafe."

- Inji wani Mustafa.

Matar aure ta sha da kyar

Wata Baiwar Allah kuwa ta ce an gwabje surukarta da bindiga a dalilin kin yarda da wasu gungun ‘yan bindiga su yi lalata da ita, da kyar ta rarrafa, ta tsira.

“Ta na wanka sai wani ‘dan bindiga ya shigo dakinta. Ya nemi ya yi mata ta'adi, ta ki yarda, sai rigima ta kicime tsakaninsu, ya buga mata bindiga.” - Surukar

Masari yace a nemi bindigogi

Gwamna Aminu Bello Masari yana ganin duk da an kara yawan ‘yan sanda, jami’an tsaron da ake da su a jihohi sun yi karanci, don haka yace kowa ya nemi makami.

Gwamnan na Katsina yace a musulunce duk wanda ya mutu yana kare kan shi ko iyalinsa, ana sa shi cikin masu shahada, don haka yace kowa ya samu bindigarsa.

Kara karanta wannan

Babu kanta yayin da ‘Yan bindiga suka dauke Mai daki, 'ya ‘yan ‘Dan Sanda a jajibirin Kirismeti

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng