Jami’an tsaro sun gaza, Gwamnan Arewa ya sake ba Talakawa shawara su tanadi bindigogi

Jami’an tsaro sun gaza, Gwamnan Arewa ya sake ba Talakawa shawara su tanadi bindigogi

  • Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya kuma bada shawara ga mutanensa su nemi makamai
  • Rt. Hon. Masari yace ba zai yiwu jama’a su zauna haka kurum ana kawo masu hari ba su da bindiga ba
  • Gwamnatin Masari za ta taimaka wajen ganin an yi wa duk bindigogi lasisi domin gudun a samu matsala

Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya yi kira ga mazauna su nemi bindigogi domin su iya kare kansu da miyagun ‘yan bindiga.

Jaridar Premium Times ta rahoto Aminu Bello Masari ya na wannan kira ne saboda jami’an tsaro kadai ba za su iya magance matsalar rashin tsaro a Katsina ba.

Da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati na Muhammadu Buhari da ke birnin Katsina, gwamnan yace jami’an tsaron da ke jihar sun yi kadan.

Kara karanta wannan

Ku sayi bindiga, ku kare kan ku: Masari ya yi kira ga al'ummar jiharsa

Kamar yadda Premium Times ta fitar da rahoto a ranar 29 ga watan Disamba, 2021, Aminu Masari yace duk wanda ya mutu wajen kare kan shi, to ya yi shahada.

Jami’an tsaro
Aminu Bello Masari da jami'an sojoji Hoto: headtopics.com
Asali: UGC

Masari ya kafa hujja da addini

“Ya halatta a musulunci mutum ya kare kan shi daga hari. Dole mutum ya tsare mutuncin kansa, iyalinsa da dukiyarsa. Idan ka mutu a haka, ka yi shahada.”
“Abin ban mamaki ne a ce mugun ‘dan bindiga ya rike bindiga, amma mutumin kirki bai da bindigar da zai kare kan shi da iyalinsa.” – Aminu Bello Masari.

Gwamnan na Katsina yace gwamnatinsa za ta taimakawa mutane mallakar bindiga, yace ‘yan sanda za su yi rajistar bindigogi domin ganin ba a wuce gona da iri ba.

Mai girma gwamnan yace ba za a zura idanu mutane su na ta mutuwa ba, yace duk da ana ta kara adadin ‘yan sanda, har yanzu adadinsu bai wadatar da kasar sosai ba.

Kara karanta wannan

A kusan karon farko, rikakken ‘Dan adawa, Sule Lamido ya yabawa matakin da Buhari ya dauka

An kashe mutane barkatai a Najeriya

Hakan na zuwa ne bayan wani rahoto ya bayyana cewa an hallaka sama da mutane 100 a makon da ya gabata yayin da lamarin tsaro ke kara tabarbarewa.

Hare-haren da aka kai a makon na jiya sun hada da mutane 20 da aka dauke a Sabon Tasha a Kaduna, sannan an kashe mutane a Faskari, jihar Katsina.

An kuma kashe mutane, an sace dabbobi a kauyukan Tungar Bai da Tungar Kade a jihar Zamfara.

Adamawa: An yi garkuwa da MOPOL

Washegarin kirismeti ne aka ji cewa tsautsayi ya sa ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani Jami’in MOPOL da ya ci kwalliyan kirismeti a kauyen Adamawa.

‘Yan Sanda su na kokarin ceto Bayin Allah da aka dauke a ranar bikin kirismeti a garin Mayo-Belwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng