‘Yan bindiga sun yi kuskure, sun yi awon gaba da Jami’in tsaro, sun dauka Attajiri su ka sace

‘Yan bindiga sun yi kuskure, sun yi awon gaba da Jami’in tsaro, sun dauka Attajiri su ka sace

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wani MOPOL a kauyen Tike, garin Mayo-Belwa, da ke jihar Adamawa

Jami’in tsaron ya ci kwalliyar kirismeti, sai ‘yan bindiga suka dauka shi ne Attajirin da su ke nema

Wannan jami’in ya na tare ne da rundunar Operation Farauta da aka kafa domin yakar ‘yan bindiga

Adamawa – Wani jami’in tsaro na MOPOL da ke tare da rundunar Operation Farauta ya fada hannun miyagun ‘yan bindiga a garin Mayo-Belwa.

Jaridar Daily Trust tace ‘yan bindiga sun aukawa yankin Mayo-Belwa ne a ranar Asabar, 25 ga watan Disamba, 2021 da kimanin kerfe 7:00 na dare.

Miyagun sun shigo Tike a kan babura, su na neman wani attajiri da ya gina katafaren gida a kauyen.

Majiya ta shaidawa manema labarai cewa da ‘yan bindigan suka iso wannan gida su na neman mai shi, sai suka yi kuskuren daukar wani jami’in tsaro.

Kara karanta wannan

Babu kanta yayin da ‘Yan bindiga suka dauke Mai daki, 'ya ‘yan ‘Dan Sanda a jajibirin Kirismeti

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wannan jami’in na MOPOL ya zuba katuwar babbar riga har kasa, ya kuma ci hula, sai ‘yan bindigan suka yi tunanin shi ne Attajirin da suke nema.

Jami’in tsaro
Wani jami'in tsaro a Najeriya
Asali: Depositphotos

Abin da ya ceci Alhaji inji 'yan gari

Mutumin da ake nema ya gina wani gida na a-zo-a gani a daidai kan hanyar Belwa zuwa Jalingo. Babban attajiri ne wanda ya saba caba ado a kullu-yaumin.

Daily Nigerian tace Alhajin ya yi sa’a, a lokacin da ‘yan bindigan suka duro cikin gida, ya yi shirin barci.

“Masu ba ‘yan bindiga bayanai sun yi masu kwatancen Alhaji Idi, a lokacin da suka iso gidan, Alhaji Idi ya cire tufafinsa, ya sa kayan barci da hula.”
“Su ka shiga tambaya, Ina mai gidan nan? Ina Alhaji? Kowa ya yi shiru, sai suka dauke MOPOL da ya ci babbar riga da hula na bikin kirismeti.”

Kara karanta wannan

Akwai hannun Gwamnoni wajen kawowa Buhari matsalar tsaro inji Tsohon Shugaban Majalisa

- Kabiru Kelly, mazaunin garin.

'Yan bindiga sun lahanta Operation Farauta

Da aka nemi a tuntubi kakakin ‘yan sand ana jihar Adamawa, Suleiman Nguroje, bai amsa waya ba. Ana sa rai ana kokarin ceto mutanen da aka sace a kauyen.

An kafa tawagar Operation Farauta ne domin kawo karshen ta’adin ‘Yan Shila da masu garkuwa da mutane a Mayo Belwa da sauran garuruwa a jihar Adamawa.

An dauke matar 'dan sanda a Kaduna

Idan ba ku manta ba, a ranar 24 ga watan Disamba, 2021, ‘Yan bindiga suka dura wata Unguwa a garin Zaria, suka rika bi gida zuwa gida su na sace Bayin Allah.

An yi rashin sa’a, an yi gaba da mata da kuma ‘ya ‘yan wani jami’in ‘yan sandan Najeriya da ke zaune a unguwar ta Wusasa a Zaria, har yanzu kuma ba su fito ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng