Ya matsa a bashi kasonsa: Matashi ya maka mahaifiyarsa a kotu kan gadon mahaifinsa, mutane sun magantu
- Wani matashi ya janyo surutai bayan ya bayar da labarin yadda abokinsa ya kai karar mahaifiyarsa kotu
- A cewar OnyedikaAnambra, mahaifin abokinsa ne ya rasu kuma ya bar mukudan dukiya, hakan ya haddasa rigima tsakaninsa da mahaifiyarsa
- Mutane da dama a kafar sada zumunta sun nuna rashin jindadinsu akan abinda yaron ya yi, yayin da wasu bisa hujjoji su ka bi bayansa
Wani matashi ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan ya wallafa wani abu da abokinsa ya aikata.
A wata wallafa da OnyedikaAnambra ya yi a kafar sada zumunta ta zamani ya bayyana yadda mahaifin shakikin abokinsa ya rasu ya bar wa iyalansa dukiya.
Shin yaron kirki ne?
Abokin nasa ya yanke shawarar maka mahaifiyarsa kotu akan dukiyar. Kamar yadda ya wallafa:
“Yanzu na samu labarin yadda wani shakikin abokina ya kai mahaifiyarsa kotu akan dukiyar da mahaifinsa ya mutu ya bari. Yaron ya na kokarin kanainaye dukiyar duk da mahaifiyarsa ta na da rai. Kada mu haifi dan banza fa a rayuwar nan.”
Legit.ng ta tattaro wasu tsokaci a karkashin wallafar
mr_cjayerus ya ce:
“Duk wata dukiya da mutum ya tara ta matarsa ce idan ya mutu, matsawar bai bayar da wasiyyar yadda za a raba dukiyar ba, a idon shari’a, ma’aurata a dunkule su ke, kamar yadda idan dukiyar ta matar ce.”
Danielchidubem7 ya ce:
“Eh nasan akwai mugayen iyaye mata amma ga yaron da har zai iya kai mahaifiyarsa kara gaban kotu, hakan na nuna cewa dama bai yi rayuwa mai kyau ba tun mahaifinsa na da rai. In ban da hakan da mahaifin ya ba dansa damar juya dukiyar tun ya na da rai, idan har da gaske yaron kirki ne.”
ugbajagonna ya kada baki ya ce:
“Na taba jin labarin yaron da ya gina gida lokacin ya na kasar waje, daga baya abubuwa su ka lalace ya dawo. Daga nan su ka fara rikici da mahaifiyarsa akan gidan da ya gina da kudinsa.”
SymplyMma ta ce:
“Mahaifiyar ce za ta ci nasara.”
ruleyourspace ya ce:
“Duk da haka sai ya biya lauya kudi. Da kamar ni ce uwar, da na ba shi kason shi. Sai in rubuta wasiyya akan kada a ba shi ko sisi idan na mutu.”
Kano: Mata ta garzaya kotun shari'a ta nemi a raba aurenta da mijinta saboda murguɗa baki
A wani labarin, mata ta maka mijin ta gaban kotu don bukatar a raba auren su sakamakon yadda rikici da tashin hankali ke aukuwa tsakanin su.
Ta bayyana gaban Alkali Munzali Tanko na kotun musulunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano don gabatar da korafin ta bisa ruwayar Dala FM.
Kamar yadda ta ce, mijin na ta ya na ci wa iyayen ta mutunci kuma ba ya ganin darajar su ko kadan kamar yadda ya zo a ruwayar na Dala FM.
Asali: Legit.ng